Zabura 83
Waƙa ce. Zabura ta Asaf.
Ya Allah, kada ka yi shiru;
kada ka tsaya cik,
ya Allah, kada ka daina motsi.
Dubi yadda abokan gābanka suke fariya,
dubi yadda maƙiyanka suke ɗaga kansu.
Da wayo suna ƙulle-ƙulle a kan mutanenka;
suna shirya maƙarƙashiya a kan waɗanda kake so.
Suna cewa, “Ku zo, bari mu hallaka su ɗungum a matsayin al’umma,
don kada a ƙara tuna da sunan Isra’ila.”
 
Da zuciya ɗaya suka yi ƙulle-ƙulle tare;
suka haɗa kai gāba da kai,
tentunan Edom da na mutanen Ishmayel,
na Mowab da kuma na Hagirawa,
Gebal, Ammon da Amalek,
Filistiya, tare da mutanen Taya.
Har Assuriya ma ta haɗa kai da su
don ta ba da ƙarfi ga zuriyar Lot.
Sela
 
Ka yi musu abin da ka yi wa Midiyan,
yadda ka yi wa Sisera da Yabin a kogin Kishon,
10 waɗanda suka hallaka a En Dor
suka zama kamar juji a ƙasa.
11 Ka mai da manyansu kamar Oreb da Zeyib,
dukan sarakunansu kamar Zeba da Zalmunna,
12 waɗanda suka ce, “Bari mu mallaki
wuraren kiwon Allah.”
 
13 Ka mai da su kamar ɗan tsiron da kan karye, iska ta yi ta turawa, ya Allahna,
kamar yayin da iska take hurawa,
14 kamar yadda wuta ke cin kurmi
ko harshen wutar da take ci a kan duwatsu,
15 haka za ka kore su da iska mai ƙarfi
ka kuma firgita su da guguwarka.
16 Ka rushe fuskokinsu da kunya
don mutane su nemi sunanka, ya Ubangiji.
 
17 Bari su kasance cikin kunya da taƙaici;
bari su hallaka cikin wulaƙanci.
18 Bari su san cewa kai, wanda sunansa ne Ubangiji,
cewa kai kaɗai ne Mafi Ɗaukaka a bisa dukan duniya.