Zabura 86
Addu’ar Dawuda.
Ka ji, ya Ubangiji, ka kuma amsa mini,
gama ni matalauci ne mai bukata kuma.
Ka tsare raina, gama na ba da kaina gare ka.
Kai ne Allahna; ka ceci bawanka
wanda ya dogara gare ka.
Ka yi mini jinƙai, ya Ubangiji,
gama na yi kira gare ka dukan yini.
Ka ba bawanka farin ciki
gama gare ka, ya Ubangiji,
na miƙa raina.
 
Kai mai gafartawa da kuma mai alheri ne, ya Ubangiji,
cike da ƙauna ga dukan waɗanda suke kira gare ka.
Ka ji addu’ata, ya Ubangiji;
ka saurari kukata na neman jinƙai.
A lokacin wahala zan yi kira gare ka,
gama za ka amsa mini.
 
A cikin alloli babu kamar ka, ya Ubangiji;
babu ayyukan da za a kwatanta da naka.
Dukan al’umman da ka yi
za su zo su yi sujada a gabanka, ya Ubangiji;
za su kawo ɗaukaka ga sunanka.
10 Gama kai mai girma ne kana kuma aikata ayyuka masu banmamaki;
kai kaɗai ne Allah.
 
11 Ka koya mini hanyarka, ya Ubangiji,
zan kuwa yi tafiya cikin gaskiyarka;
ka ba ni zuciya wadda ba tă rabu ba,
don in ji tsoron sunanka.
12 Zan yabe ka, ya Ubangiji Allahna, da dukan zuciyata;
zan ɗaukaka sunanka har abada.
13 Gama ƙaunarka da girma take gare ni;
kai ka cece ni daga zurfafa,
daga mazaunin matattu.
 
14 Masu girman kai suna kai mini hari, ya Allah;
ƙungiyar marasa imani suna neman raina,
mutanen da ba su kula da kai ba.
15 Amma kai, ya Ubangiji, kai Allah mai tausayi ne da kuma mai alheri,
mai jinkirin fushi, mai yawan ƙauna da aminci.
16 Ka juyo gare ni ka yi mini jinƙai;
ka ba wa bawanka ƙarfi;
ka ceci ni gama na bauta maka
yadda mahaifiyata ta yi.
17 Ka ba ni alamar alherinka,
don abokan gābana su gani su kuma sha kunya,
gama kai, ya Ubangiji, ka taimake ni ka kuma ta’azantar da ni.