Zabura 87
Na ’ya’yan Kora maza. Zabura ce. Waƙa ce.
Ya kafa harsashinsa a kan dutse mai tsarki.
Ubangiji yana ƙaunar ƙofofin Sihiyona
fiye da dukan wuraren zaman Yaƙub.
 
Ana faɗin abubuwa masu ɗaukaka game da ke
Ya birnin Allah,
Sela
“Zan lissafta Rahab
a cikin waɗanda suka san ni,
Filistiya ita ma, da Taya, tare da Kush,
zan kuma ce, ‘An haifi wannan a Sihiyona.’ ”
Tabbatacce, game da Sihiyona za a ce,
“Wannan da wancan an haifa a cikinta,
Mafi Ɗaukaka kansa zai kafa ta.”
Ubangiji zai rubuta a littafin sunayen mutanensa,
“An haifi wannan a Sihiyona.”
Sela
 
Yayinda suke kaɗe-kaɗe za su rera,
“Dukan maɓulɓulaina suna cikinki.”