Zabura 94
Ya Ubangiji, Allahn da yake ramuwa,
Ya Allah wanda yake ramuwa, ka haskaka.
Ka tashi, ya Alƙalin duniya;
ka sāka wa masu girman kai abin da ya dace da su.
Har yaushe mugaye, ya Ubangiji
har yaushe mugaye za su yi ta murna?
 
Suna ta yin maganganun fariya;
dukan masu aikata mugunta sun cika da fariya.
Suna murƙushe mutanenka, ya Ubangiji;
suna danne gādonka.
Suna kashe gwauraye da kuma baƙi;
suna kisan marayu.
Suna ce, “Ubangiji ba ya gani;
Allah na Yaƙub bai kula ba.”
 
Ku mai da hankali, ku marasa azanci a cikin mutane;
ku wawaye, yaushe za ku zama masu hikima?
Shi da ya sa kunne ba don a ji ba ne?
Shi da ya yi ido ba don yă gani ba ne?
10 Shi da yake yi wa al’ummai horo ba ya hukunci ne?
Shi da yake koya wa mutum ba shi da sani ne?
11  Ubangiji ya san tunanin mutum;
ya san cewa tunaninsu banza ne.
 
12 Mai albarka ne mutumin da ka yi masa horo, ya Ubangiji,
mutumin da ka koyar daga dokarka;
13 kana ba shi sauƙi a lokacin wahala,
sai har an haƙa rami wa mugaye.
14 Gama Ubangiji ba zai ƙi mutanensa ba;
ba zai taɓa yashe gādonsa ba.
15 Za a sāke kafa hukunci a kan adalci,
kuma dukan masu adalci a zuciya za su bi shi.
 
16 Wane ne zai yi gāba da mugaye domina?
Wane ne zai ɗauki matsayi ya yi gāba da masu aikata mugunta domina?
17 Da ba don Ubangiji ya yi mini taimako ba,
da tuni na zauna shiru a wurin mutuwa.
18 Sa’ad da na ce, “Ƙafata na santsi,”
ƙaunarka, ya Ubangiji, ta riƙe ni.
19 Sa’ad da alhini ya yi yawa a cikina,
ta’aziyyarka ta kawo farin ciki wa raina.
 
20 Zai yiwu kursiyin da ya cika da lalaci yă haɗa kai da kai,
wanda yake kawo azaba ta wurin abin da ya zartar?
21 Sun yi ƙungiya tare a kan mai adalci
suka yanke wa marar laifi hukuncin mutuwa.
22 Amma Ubangiji ya zama kagarata,
Allahna kuma dutsen da nake samun mafaka.
23 Zai sāka musu saboda zunubansu
yă kuma hallaka su saboda muguntarsu;
Ubangiji Allahnmu zai hallaka su.