Zabura 95
Ku zo, bari mu rera don farin ciki ga Ubangiji;
bari mu yi sowa da ƙarfi ga Dutsen cetonmu.
Bari mu zo gabansa da godiya
mu rera gare shi da kiɗi da waƙa.
 
Gama Ubangiji Allah mai girma ne,
babban Sarki a bisa dukan alloli.
A hannunsa ne zurfafan duniya suke,
ƙwanƙolin dutse kuma nasa ne.
Teku nasa ne, gama shi ne ya yi shi,
da hannuwansa kuma ya yi busasshiyar ƙasa.
 
Ku zo, bari mu rusuna mu yi sujada,
bari mu durƙusa a gaban Ubangiji Mahaliccinmu;
gama shi ne Allahnmu
mu mutanen makiyayansa ne,
garke kuwa a ƙarƙashin kulawarsa.
 
Yau, in kuka ji muryarsa,
“Kada ku taurare zukatanku kamar yadda kuka yi a Meriba,*
kamar yadda kuka yi a wancan rana a Massa a hamada,
inda kakanninku suka gwada suka kuma jarraba ni,
ko da yake sun ga abin da na yi.
10 Shekara arba’in na yi fushi da wancan tsara;
na ce, ‘Su mutane ne waɗanda zukatansu suka kauce,
kuma ba su san hanyoyina ba.’
11 Saboda haka na yi rantsuwa cikin fushina,
‘Ba za su taɓa shiga hutuna ba.’ ”
* Zabura 95:8 Meriba yana nufin faɗa. Zabura 95:8 Massa yana nufin gwaji.