Zabura 99
Ubangiji yana mulki,
bari al’ummai su yi rawan jiki;
yana zaune a kursiyi tsakanin kerubobi,
bari duniya ta girgiza.
Ubangiji mai girma yana a Sihiyona;
an ɗaukaka shi a bisa dukan al’ummai.
Bari mu yabi girmanka da sunanka mai banrazana,
shi mai tsarki ne.
 
Sarki mai iko ne, yana ƙaunar adalci
ka kafa gaskiya;
a cikin Yaƙub ka yi
abin da yake mai adalci da kuma daidai.
Ku ɗaukaka Ubangiji Allahnmu
ku kuma yi masa sujada a wurin sa ƙafafunsa;
shi mai tsarki ne.
 
Musa da Haruna suna cikin firistocinsa,
Sama’ila yana cikin waɗanda suka kira bisa sunansa;
sun kira ga Ubangiji
ya kuwa amsa musu.
Ya yi magana da su daga ginshiƙin girgije;
ya kiyaye farillansa da ƙa’idodin da ya ba su.
 
Ya Ubangiji Allahnmu,
ka amsa musu;
ka kasance wa Isra’ila Allah mai gafartawa,
ko da yake ka hukunta ayyukansu marasa kyau.
Ku ɗaukaka Ubangiji Allahnmu
ku kuma yi sujada a dutsensa mai tsarki,
gama Ubangiji Allahnmu mai tsarki ne.