Zabura 98
Zabura ce.
Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji,
gama ya yi abubuwa masu banmamaki;
hannunsa na dama da hannunsa mai tsarki
sun yi masa aikin ceto.
Ubangiji ya sanar da cetonsa
ya kuma bayyana adalcinsa ga al’ummai.
Ya tuna da ƙaunarsa
da kuma amincinsa ga gidan Isra’ila;
dukan iyakar duniya sun ga
ceton Allahnmu.
 
Ku yi sowa don farin ciki ga Ubangiji, dukan duniya,
ku ɓarke da waƙa ta murna tare da kiɗi;
ku yi kiɗi ga Ubangiji da garaya,
da garaya da ƙarar rerawa,
tare da bushe-bushe da karar ƙahon rago,
ku yi sowa don farin ciki a gaban Ubangiji, Sarki.
 
Bari teku su yi ruri, da kuma kome da yake cikinsa,
duniya da kuma kome da yake cikinta.
Bari koguna su tafa hannuwansu,
bari duwatsu su rera tare don farin ciki;
bari su rera a gaban Ubangiji,
gama yana zuwa domin yă hukunta duniya.
Zai hukunta duniya da adalci
mutane kuma cikin gaskiya.