5
Zuriyar Ruben
’Ya’yan Ruben maza ɗan farin Isra’ila (shi ne ɗan fari, amma sa’ad da ya ƙazantar da gadon auren mahaifinsa, sai aka ba wa ’yancin ɗan farinsa wa ’ya’yan Yusuf maza ɗan Isra’ila; don kada a lissafta shi a tarihin zuriya bisa ga matsayin haihuwarsa, ko da yake Yahuda shi ne mafi ƙarfi cikin ’yan’uwansa kuma mai mulki ya fito daga gare shi, ’yancin zaman ɗan fari na Yusuf ne), ’ya’yan Ruben ɗan farin Isra’ila maza su ne,
 
Hanok, Fallu, Hezron da Karmi.
Zuriyar Yowel su ne,
Shemahiya, Gog,
Shimeyi, Mika,
Reyahiya, Ba’al,
da Beyera, wanda Tiglat-Fileser sarkin Assuriya ya ɗauka zuwa zaman bauta. Beyera shi ne shugaban mutanen Ruben.
Danginsu bisa ga iyalansu da aka jera bisa ga tarihin zuriyarsu su ne,
Yehiyel shi ne sarki, akwai Zakariya, da Bela ɗan Azaz. Azaz ɗan Shema daga dangin Yowel.
 
Yowel ya yi zama a yankin Arower har zuwa Nebo da Ba’al-Meyon. Ta waje gabas sun zauna a ƙasar har zuwa bakin hamadan da ya nausa zuwa Kogin Yuferites, domin dabbobinsu sun ƙaru a Gileyad.
10 A zamanin Shawulu zuriyar Ruben sun yi yaƙi da Hagirawa, suka ci su da yaƙi, suka zauna a wuraren zaman Hagirawan ko’ina a dukan yankin gabashin Gileyad.
Zuriyar Gad
11 Mutanen Gad sun zauna kusa da mutanen Ruben a Bashan, har zuwa Saleka.
 
12 Yowel shi ne babba, sai Shafan na biyu, sa’an nan Yanai da Shafat, su ne tushen Bashan.
13 Danginsu, bisa ga iyalai su ne,
Mika’ilu, Meshullam, Sheba, Yorai, Yakan, Ziya da Eber, su bakwai ne duka.
14 Waɗannan su ne ’ya’yan Abihayil ɗan Huri, ɗan Yarowa, ɗan Gileyad, ɗan Mika’ilu, ɗan Yeshishai, ɗan Yado, ɗan Buz.
15 Ahi ɗan Abiyel, ɗan Guni, shi ne kan iyalinsu.
 
16 Mutanen Gad sun zauna a Bashan da ƙauyukan da suke kurkusa da shi, da kuma a dukan makiyayan Sharon har zuwa iyaka inda suka kai.
17 Dukan waɗannan sun shiga tarihin zuriya a lokacin mulkin Yotam sarkin Yahuda da Yerobowam sarkin Isra’ila.
 
18 Mutanen Ruben, mutanen Gad da rabin kabilar Manasse sun kasance da mutane 44,760 shiryayyu don aikin soja, jarumawan da za su iya riƙe garkuwa da takobi, waɗanda suke iya yin amfani da baka, waɗanda kuma aka horar don yaƙi. 19 Suka yi yaƙi da Hagirawa, Yetur, Nafish da Nodab. 20 Aka taimake su a yaƙin, Allah kuma ya ba da Hagirawa da dukan abokansu gare su, domin sun yi kuka gare shi a lokacin yaƙin. Ya amsa addu’o’insu, domin sun dogara gare shi. 21 Suka ƙwace dabbobin Hagirawa, raƙuma dubu hamsin, tumaki dubu ɗari biyu da hamsin da kuma jakuna dubu biyu. Suka kuma kame mutane dubu ɗari ɗaya, 22 waɗansu suka mutu, domin yaƙin na Allah ne. Suka zauna a ƙasar har lokacin da aka kai su zaman bauta.
Rabin kabilar Manasse
23 Mutanen rabin kabilar Manasse sun yi yawa; suka zauna a ƙasar daga Bashan har zuwa Ba’al-Hermon, wato, zuwa Senir (Dutsen Hermon).
24 Waɗannan su ne kawunan iyalansu. Efer, Ishi, Eliyel, Azriyel, Irmiya, Hodawiya da Yadiyel. Su jarumawa ne, sanannu, su ne kuma kawunan iyalansu. 25 Amma ba su yi aminci da Allahn kakanninsu ba, suka kuma yi karuwanci ga waɗansu allolin mutanen ƙasar, waɗanda Allah ya hallaka a gabansu. 26 Saboda haka Allah na Isra’ila ya zuga ruhun Ful sarkin Assuriya (wato, Tiglat-Fileser sarkin Assuriya), wanda ya kwashe mutanen Ruben, mutanen Gad da rabin kabilar Manasse zuwa zaman bauta. Ya kwashe su zuwa Hala, Habor, Hara da kuma kogin Gozan, inda suke har wa yau.