6
Zuriyar Lawi
1 ’Ya’yan Lawi maza su ne,
Gershon, Kohat da Merari.
2 ’Ya’yan Kohat maza su ne,
Amram, Izhar, Hebron da Uzziyel.
3 Yaran Amram su ne,
Haruna, Musa da Miriyam.
’Ya’yan Haruna maza su ne,
Nadab, Abihu, Eleyazar da Itamar.
4 Eleyazar shi ne mahaifin Finehas,
Finehas mahaifin Abishuwa,
5 Abishuwa mahaifin Bukki,
Bukki mahaifin Uzzi,
6 Uzzi mahaifin Zerahiya,
Zerahiya mahaifin Merahiyot,
7 Merahiyot mahaifin Amariya,
Amariya mahaifin Ahitub,
8 Ahitub mahaifin Zadok,
Zadok mahaifin Ahimawaz,
9 Ahimawaz mahaifin Azariya,
Azariya mahaifin Yohanan,
10 Yohanan mahaifin Azariya (shi ne ya yi hidima a matsayin firist a haikalin da Solomon ya gina a Urushalima),
11 Azariya mahaifin Amariya,
Amariya mahaifin Ahitub,
12 Ahitub mahaifin Zadok,
Zadok mahaifin Shallum,
13 Shallum mahaifin Hilkiya,
Hilkiya mahaifin Azariya,
14 Azariya mahaifin Serahiya,
Serahiya kuwa mahaifin Yehozadak.
15 Yehozadak ne aka ɗauka sa’ad da Ubangiji ya tura Yahuda da Urushalima zuwa zaman bauta ta hannun Nebukadnezzar.
16 ’Ya’yan Lawi maza su ne,
Gershom, Kohat da Merari.
17 Waɗannan su ne sunayen ’ya’yan Gershom.
Libni da Shimeyi.
18 ’Ya’yan Kohat maza su ne,
Amram, Izhar, Hebron da Uzziyel.
19 ’Ya’yan Merari maza su ne,
Mali da Mushi.
Waɗannan suke gidajen Lawiyawan da aka jera bisa ga kakanninsu.
20 Na Gershom su ne,
Libni, Yahat,
Zimma,
21 Yowa,
Iddo, Zera
da Yeyaterai.
22 Zuriyar Kohat su ne,
Amminadab, Kora,
Assir,
23 Elkana,
Ebiyasaf, Assir,
24 Tahat, Uriyel,
Uzziya da Shawulu.
25 Zuriyar Elkana su ne,
Amasai, Ahimot,
26 Elkana, Zofai,
Nahat,
27 Eliyab
Yeroham, Elkana
da Sama’ila.
28 ’Ya’yan Sama’ila maza su ne,
Yowel ɗan fari
da Abiya ɗa na biyu.
29 Zuriyar Merari su ne,
Mali, Libni,
Shimeyi, Uzza,
30 Shimeya, Haggiya
da Asahiya.
Mawaƙan haikali
31 Waɗannan su ne mutanen da Dawuda ya sa su lura da waƙa a cikin gidan Ubangiji bayan da aka kawo akwatin alkawari yă huta a can.
32 Suka yi hidima da waƙa a gaban tabanakul, Tentin Sujada, sai da Solomon ya gina haikalin Ubangiji a Urushalima. Suka yi ayyukansu bisa ga ƙa’idodin da aka shimfiɗa musu.
33 Ga mutanen da suka yi hidimar, tare da ’ya’yansu maza.
Daga mutanen Kohat akwai,
Heman, mawaƙi
ɗan Yowel, ɗan Sama’ila,
34 ɗan Elkana, ɗan Yeroham,
ɗan Eliyel, ɗan Towa,
35 ɗan Zuf, ɗan Elkana,
ɗan Mahat, ɗan Amasai,
36 ɗan Elkana, ɗan Yowel,
ɗan Azariya, ɗan Zefaniya
37 ɗan Tahat, ɗan Assir,
ɗan Ebiyasaf, ɗan Kora,
38 ɗan Izhar, ɗan Kohat,
ɗan Lawi, ɗan Isra’ila;
39 da kuma Asaf ’yan’uwan Heman, waɗanda suka yi hidima a hannun damansa.
Asaf ɗan Berekiya, ɗan Shimeya,
40 ɗan Mika’ilu, ɗan Ba’asehiya,
ɗan Malkiya,
41 ɗan Etni,
ɗan Zera, ɗan Adahiya
42 ɗan Etan, ɗan Zimma,
ɗan Shimeyi,
43 ɗan Yahat,
ɗan Gershom, ɗan Lawi;
44 da kuma daga ’yan’uwansu, mutanen Merari, a hannun hagunsa.
Etan ɗan Kishi, ɗan Abdi,
ɗan Malluk,
45 ɗan Hashabiya,
ɗan Amaziya, ɗan Hilkiya,
46 ɗan Amzi, ɗan Bani,
ɗan Shemer,
47 ɗan Mali,
ɗan Mushi, ɗan Merari,
ɗan Lawi.
48 Aka ba ’yan’uwansu Lawiyawa dukan sauran ayyukan tabanakul, gidan Allah.
49 Amma Haruna da zuriyarsa su ne waɗanda suke miƙa hadayu a kan bagaden hadaya ta ƙonawa da kuma a kan bagaden turare haɗe da dukan abin da ake yi a Wuri Mafi Tsarki, suna yin kafara domin Isra’ila, bisa ga dukan abin da Musa bawan Allah ya umarta.
50 Waɗannan su ne zuriyar Haruna,
Eleyazar, Finehas,
Abishuwa,
51 Bukki,
Uzzi, Zerahiya,
52 Merahiyot, Amariya,
Ahitub,
53 Zadok
da Ahimawaz.
(Yoshuwa 21.1-42)
54 Waɗannan su ne wuraren zamansu da aka ba su rabo su zama yankunansu (aka ba wa zuriyar Haruna waɗanda suke daga gidan Kohat, domin rabo na fari nasu ne):
55 Aka ba su Hebron a Yahuda tare da wuraren kiwon da suke kewayenta.
56 Amma filaye da ƙauyukan da suke kewayen birnin aka ba wa Kaleb ɗan Yefunne.
57 Saboda haka aka ba wa zuriyar Haruna Hebron (birnin mafaka), da Libna, Yattir Eshtemowa,
58 Hilen, Debir,
59 Ashan, Yutta da Bet-Shemesh, tare da wuraren kiwonsu.
60 Daga kabilar Benyamin kuma aka ba su Gibeyon, Geba, Alemet da Anatot, tare da wuraren kiwonsu.
Waɗannan garuruwa waɗanda aka raba a tsakanin mutanen gidan Kohat, goma sha uku ne duka.
61 Aka ba sauran zuriyar Kohat rabon garuruwa goma daga gidajen rabin kabilar Manasse.
62 Aka ba zuriyar Gershom, gida-gida, rabon garuruwa goma sha uku daga kabilan Issakar, Asher da Naftali, da kuma daga sashen rabi kabilar Manasse da yake a Bashan.
63 Aka ba zuriyar Merari, gida-gida, rabon garuruwa goma sha biyu daga kabilan Ruben, Gad da Zebulun.
64 Saboda haka Isra’ilawa suka ba Lawiyawa waɗannan garuruwa da wuraren kiwonsu.
65 Daga kabilan Yahuda, Simeyon da Benyamin suka ba su rabon sunayen garuruwan da aka ambata.
66 Aka ba wa waɗansu na mutanen gidan Kohat yankin garuruwansu daga kabilar Efraim.
67 A ƙasar tudun Efraim aka ba su Shekem (birnin mafaka), da Gezer,
68 Yokmeyam, Bet-Horon,
69 Aiyalon da Gat-Rimmon, tare da wuraren kiwonsu.
70 Daga rabin kabilar Manasse kuwa, Isra’ilawa suka ba da Aner da Bileyam, tare da wuraren kiwonsu, ga sauran gidajen mutanen Kohat.
71 Mutanen Gershom suka sami waɗannan.
Daga gidan rabin kabilar Manasse, sun sami Golan a Bashan da kuma Ashtarot, tare da wuraren kiwonsu;
72 daga kabilar Issakar suka sami Kedesh, Daberat,
73 Ramot da Anem, tare da wuraren kiwonsu;
74 daga kabilar Asher suka sami Mashal, Abdon,
75 Hukok da Rehob, tare da wuraren kiwonsu;
76 daga kabilar Naftali kuwa suka sami Kedesh a Galili, Hammon da Kiriyatayim, tare da wuraren kiwonsu.
77 Mutanen Merari (sauran Lawiyawan) suka sami waɗannan.
Daga kabilar Zebulun suka sami Yokneyam, Karta, Rimmon da Tabor, tare da wuraren kiwonsu;
78 daga kabilar Ruben a hayin Urdun a gabashi Yeriko suka sami Bezer a hamada, Yahza,
79 Kedemot da Mefa’at, tare da wuraren kiwonsu;
80 daga kabilar Gad kuwa suka sami Ramot a Gileyad, Mahanayim,
81 Heshbon da Yazer, tare da wuraren kiwonsu.