7
Zuriyar Issakar
1 ’Ya’yan Issakar maza su ne,
Tola, Fuwa, Yashub da Shimron, su huɗu ne duka.
2 ’Ya’yan Tola maza su ne,
Uzzi, Refahiya, Yeriyel, Ibsam da Sama’ila, su ne kuma kawunan iyalansu. A zamanin mulkin Dawuda, an rubuta zuriyar Tola a matsayin mayaƙa a cikin tarihinsu, sun kai 22,600.
3 Ɗan Uzzi shi ne,
Izrahiya.
’Ya’yan Izrahiya maza su ne,
Mika’ilu, Obadiya, Yowel da Isshiya. Dukansu biyar manya ne.
4 Bisa ga tarihin iyalinsu, sun kai mutane 36,000 shiryayyu don yaƙi, gama suna da mata da ’ya’ya da yawa.
5 Dangin da suke maza masu yaƙi sun kasance na dukan gidajen Issakar ne, kamar yadda aka rubuta a cikin tarihi, su 87,000 ne duka.
Zuriyar Benyamin
6 ’Ya’ya uku maza na Benyamin su ne,
Bela, Beker da Yediyayel.
7 ’Ya’yan Bela maza su ne,
Ezbon, Uzzi, Uzziyel, Yerimot da Iri, su ne kawunan iyalai, kuma su biyar ne duka. Rubutaccen tarihin zuriyarsu ya nuna suna mazan da sun isa yaƙi 22,034.
8 ’Ya’yan Beker maza su ne,
Zemira, Yowash, Eliyezer, Eliyohenai, Omri, Yeremot, Abiya, Anatot da Alemet. Dukan waɗannan ’ya’yan Beker maza ne.
9 Rubutaccen tarihin zuriyarsu ya nuna suna da kawunan iyalai da mazan da suka isa yaƙi 20,200.
10 Ɗan Yediyayel shi ne,
Bilhan.
’Ya’yan Bilhan maza su ne,
Yewush, Benyamin, Ehud, Kena’ana, Zetan, Tarshish da Ahishahar.
11 Dukan waɗannan ’ya’yan Yediyayel maza kawunan iyalai ne. Akwai mazan da suka isa yaƙi waje 17,200.
12 Shuffiyawa da Huffiyawa zuriyar Ir ne, kuma Hushiyawa zuriyar Aher ne.
Zuriyar Naftali
13 ’Ya’yan Naftali maza su ne,
Yaziyel, Guni, Yezer da Shallum, su zuriyar Bilha ne.
Zuriyar Manasse
14 Zuriyar Manasse su ne,
Asriyel zuriyarsa ne ta wurin ƙwarƙwararsa mutuniyar Aram. Ta haifa wa Makir mahaifin Gileyad.
15 Makir ya auri mata daga cikin Huffiyawa da Shuffiyawa. ’Yar’uwarsa ita ce Ma’aka. Wani daga zuriyar, sunansa Zelofehad, shi yana da ’ya’yan mata ne kawai.
16 Ma’aka matar Makir ta haifi ɗa ta kuma ba shi suna Feresh. Sunan ɗan’uwansa Sheresh, ’ya’yan Feresh maza kuwa su ne Ulam da Rakem.
17 Ɗan Ulam shi ne,
Bedan.
Duka waɗannan zuriyar Gileyad ne. Gileyad ɗan Makir ne, Makir kuma ɗan Manasse.
18 ’Yar’uwarsa Makir mai suna Hammoleket ta haifi Ishod, Abiyezer da Mala.
19 ’Ya’yan Shemida maza su ne,
Ahiyan, Shekem, Liki da Aniyam.
Zuriyar Efraim
20 Zuriyar Efraim su ne,
Shutela, Bered,
Tahat, Eleyada,
Tahat
21 Zabad
da Shutela.
Wani ɗan ƙasa haifaffen mutanen Gat ya kashe Ezer da Elad, sa’ad da suka gangara don su ƙwace dabbobinsu.
22 Mahaifinsu Efraim ya yi makoki dominsu kwanaki masu yawa sai danginsa suka zo don su yi masa ta’aziyya.
23 Sa’an nan ya sāke kwana da matarsa, sai ta yi ciki ta haifi ɗa. Ya ba shi suna Beriya, saboda masifar da ta auko a cikin iyalinsa.
24 ’Yarsa ita ce Sheyera, wadda ta gina Bet-Horon na kwari da na tudu da kuma Uzzen-Sheyera. Zuriyarsa ita ce,
25 Refa, Reshef,
Tela, Tahan,
26 Ladan, Ammihud,
Elishama,
27 Nun
da kuma Yoshuwa.
28 Ƙasarsu da wuraren zamansu sun haɗa da Betel da ƙauyukan kewayenta, Na’aran wajen gabas, Gezer da ƙauyukanta wajen yamma, da kuma Shekem da ƙauyukan da suka nausa har zuwa Aiya da ƙauyukanta.
29 A iyakokin Manasse akwai Bet-Sheyan, Ta’anak, Megiddo da Dor, tare da ƙauyukansu. Zuriyar Yusuf ɗan Isra’ila ta zauna a waɗannan garuruwa.
Zuriyar Asher
30 ’Ya’yan Asher maza su ne,
Imna, Ishba, Ishwi da Beriya. ’Yar’uwarsa ita ce Sera.
31 ’Ya’yan Beriya maza su ne,
Heber da Malkiyel, wanda yake mahaifin Birzayit.
32 Heber shi ne mahaifin Yaflet, Shomer da Hotam da kuma ’yar’uwarsu Shuwa.
33 ’Ya’yan Yaflet maza su ne,
Fasak, Bimhal da Ashwat.
Waɗannan su ne ’ya’yan Yaflet maza.
34 ’Ya’yan Shemer maza su ne,
Ahi, Roga, Yehubba da Aram.
35 ’Ya’yan ɗan’uwansa Helem su ne,
Zofa, Imna, Shelesh da Amal.
36 ’Ya’yan Zofa maza su ne,
Suwa, Harnefer, Shuwal, Beri, Imra,
37 Bezer, Hod, Shamma, Shilsha, Itran da Bera.
38 ’Ya’yan Yeter maza su ne,
Yefunne, Fisfa da Ara.
39 ’Ya’yan Ulla maza su ne,
Ara, Hanniyel da Riziya.
40 Dukan waɗannan zuriyar Asher ne, kawunan iyalai, zaɓaɓɓun mutane, jarumawa sosai da kuma fitattun shugabanni. Yawan mutanen da suke a shirye don yaƙi, kamar yadda aka lissafta zuriyarsu, 26,000 ne.