12
Jawabin bankwanan Sama’ila
Sama’ila ya ce wa Isra’ilawa duka, “Na saurari abubuwan da kuka faɗa mini, na kuma naɗa muku sarki. Yanzu kuna da sarki a matsayin shugaba, ni kuwa na tsufa har da furfura, yarana maza kuma suna tare da ku. Na yi shugabancinku tun ina yaro. Ga ni a gabanku. Idan na yi wani abin da ba daidai ba sai ku faɗa a gaban Ubangiji, da gaban sarkin da ya keɓe. Ko na taɓa ƙwace saniya ko jakin wani? Ko na taɓa cuce wani, ko in danne hakkinsa? Ko na taɓa cin hanci daga hannun ɗayanku? Idan na taɓa yi ɗaya daga cikin waɗannan, sai ku faɗa mini, zan kuwa mayar masa.”
Suka ce, “Ba ka cuci ko danne hakkin kowa ba, ba ka ƙwace kome daga hannun kowa ba.”
Sama’ila ya ce musu, “Ubangiji yă zama shaida a kanku, shafaffensa kuma yă zama shaida a wannan rana cewa ba ku same ni da wani laifin kome ba.”
Suka ce, “I, shi ne shaida.”
Sa’an nan Sama’ila ya ce wa mutane, Ubangiji ne ya naɗa Musa da Haruna suka fitar da kakanninku daga Masar. Yanzu ku tsaya nan zan yi fito-na-fito da ku da shaida a gaban Ubangiji kan dukan ayyuka masu alherin da Ubangiji ya aikata saboda ku da kakanninku.
Bayan da Yaƙub da ’ya’yansa suka shiga Masar suka yi kukan neman taimako daga Ubangiji, Ubangiji kuwa ya aika musu da Musa da Haruna. Su ne suka kawo kakanni-kakanninku daga Masar suka zauna a nan.
Amma suka manta da Ubangiji Allahnsu, shi kuma ya bashe su a hannun Sisera shugaban rundunar Hazor da kuma hannun Filistiyawa da sarkin Mowab wanda suka yi yaƙi da su. 10 Suka yi kuka a gaban Ubangiji suka ce, “Mun yi zunubi mun bar Ubangiji, muka bauta wa Ba’al da Ashtarot. Amma ka cece mu yanzu daga hannun abokan gābanmu, mu kuwa za mu bauta maka.” 11 Sai Ubangiji ya aiki Yerub-Ba’al da Bedan da Yefta da Sama’ila, ya cece ku daga hannun abokan gābanku a kowane gefe domin ku sami cikakken zaman lafiya.
12 Amma da kuka ga Nahash sarkin Ammonawa yana matsowa yă yaƙe, sai kuka ce mini, “Sam, muna so sarki yă shugabance mu.” Ko da yake Ubangiji Allahnku ne yake mulkinku. 13 Yanzu ga sarkinku da kuka zaɓa wanda kuka nema, ga shi Ubangiji ya naɗa muku sarki. 14 In kuka ji tsoron Ubangiji, kuka bauta masa, kuka yi masa biyayya, ba ku kuwa ƙi bin umarninsa ba, in kuma ku da sarkin da yake mulkinku kun bi Ubangiji Allahnku, to, za ku zauna lafiya. 15 Amma in ba ku yi biyayya ga Ubangiji ba, in kuma kuka ƙi bin umarnansa, fushinsa zai zauna a kanku.
16 Yanzu ku tsaya tsit ku ga abin da Ubangiji ke dab da yi a gabanku. 17 Ba lokacin yankan alkama ke nan ba? Zan roƙi Ubangiji yă aiko da tsawa da ruwan sama, za ku kuwa gane wace irin mugunta kuka yi a gaban Ubangiji sa’ad da kuka roƙa a ba ku sarki.
18 Sai Sama’ila ya roƙi Ubangiji, a ranar kuwa Ubangiji ya aiko da tsawa da ruwan sama. Dukan mutane suka ji tsoron Ubangiji da kuma Sama’ila.
19 Dukan mutane suka ce wa Sama’ila, “Ka yi addu’a ga Ubangiji Allahnka saboda bayinka, domin kada mu mutu, gama mun ƙara wa kanmu zunubi da muka roƙa a yi mana sarki.”
20 Sama’ila ya ce, “Kada ku ji tsoro.” Kun yi waɗannan mugunta duk da haka kada ku bar bin Ubangiji, amma ku bauta wa Ubangiji da dukan zuciyarku. 21 Kada ku bi alloli marasa amfani. Ba za su iya yi muku kome nagari ba, ba kuwa za su iya cece ku ba, gama ba su da amfani. 22 Saboda suna mai girma da Ubangiji yake da shi, ba zai taɓa ƙin mutanensa ba. Gama Ubangiji ya ji daɗi da ya yi ku mutanensa. 23 Ni kam ba zai taɓa yiwu in yi wa Ubangiji zunubi ta wurin ƙin yin addu’a dominku ba. Zan koya muku hanyar da tana da kyau da ta kuma cancanta. 24 Amma ku amince za ku ji tsoron Ubangiji, ku bauta masa da aniya da dukan zuciyarku, kuna da manyan abubuwan da ya yi muku. 25 Amma in kuka duƙufa cikin aikin mugunta da ku da sarkinku za a hallaka ku.