13
Sama’ila ya kwaɓi Shawulu
Shawulu yana da shekara talatin sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi sarautar Isra’ila shekara arba’in da biyu.
Sai ya zaɓi sojoji dubu uku daga jama’ar Isra’ila. Ya keɓe dubu biyu su kasance tare da shi a Mikmash da kuma a tuddan yankin Betel. Ya kuma bar dubu ɗaya tare da ɗansa Yonatan a Gibeya a yankin zuriyar Benyamin. Sauran sojojin kuwa Shawulu ya sallame su su koma gidajensu.
Yonatan ya kai wa Filistiyawa hari a Geba, sai Filistiyawa suka sami labarin. Sai Shawulu ya sa aka busa ƙaho ko’ina a ƙasar ya ce, “Bari Ibraniyawa su ji!” Haka kuwa dukan Isra’ila suka ji labari cewa, “Shawulu ya kai hari a ƙasar Filistiyawa, yanzu Isra’ila ta zama abin ƙi ga Filistiyawa.” Aka kira mutane su haɗu da Shawulu a Gilgal.
Sai Filistiyawa suka taru don su yi yaƙi da Isra’ilawa. Suka fito da kekunan-dawakan yaƙi dubu talatin, da masu hawan dawakai dubu shida, da sojoji masu yawa kamar yashi a bakin teku. Suka tafi Mikmash a gabashin Bet-Awen, suka kafa sansani a can. Sa’ad da Filistiyawa suka fāɗa wa Isra’ilawa da yaƙi mai tsanani, suka sa su cikin wani hali mai wuya, sai Isra’ilawa suka ɓuya a kogwanni, da ciyayi, da duwatsu, da ramummuka, da rijiyoyi. Waɗansunsu ma suka haye Urdun zuwa ƙasar Gad da Gileyad.
Shawulu ya zauna Gilgal, dukan ƙungiyoyi sojojin da suke tare da shi suka yi rawan jiki don tsoro. Ya jira har kwana bakwai bisa ga lokacin da Sama’ila ya bayar. Amma Sama’ila bai zo Gilgal ba, mutanen Shawulu suka fara watsewa. Sai ya ce, “Ku kawo mini hadaya ta ƙonawa da hadaya ta salama.” Sai Shawulu ya miƙa hadaya ta ƙonawa. 10 Daidai yana gama miƙa hadaya ke nan sai Sama’ila ya iso. Shawulu kuma ya fito domin yă yi masa maraba.
11 Sama’ila ya ce, “Me ke nan ka yi?”
Shawulu ya ce, “Sa’ad da na ga mutane suna watsewa, kai kuwa ba ka zo cikin lokaci ba, ga Filistiyawa kuma suna taruwa a Mikmash, 12 sai na yi tunani cewa, ‘Yanzu Filistiyawa za su gangaro su fāɗa mini a Gilgal, ga ni kuma ban riga na nemi nufin Ubangiji ba.’ Shi ya sa ya zama mini tilas in miƙa hadaya ta ƙonawa.”
13 Sama’ila ya ce, “Ka yi wauta da ba ka bi umarnin da Ubangiji Allahnka ya ba ka ba. Da ka yi haka da Ubangiji ya tabbatar maka da sarautar Isra’ila har abada. 14 Amma yanzu, masarautarka ba za tă dawwama ba, Ubangiji ya riga ya sami wani wanda zuciyarsa ke ƙauna, ya naɗa shi shugaban mutanensa gama ba ka bi umarnin Ubangiji ba.”
15 Sama’ila ya tashi daga Gilgal ya tafi Gibeya a ƙasar Benyamin. Shawulu kuma ya ƙidaya mutanen da suke tare da shi, yawansu ya kai wajen mutum ɗari shida.
Isra’ila ba ta da makamai
16 Shawulu da ɗansa Yonatan da mutanen da suke tare da shi suka zauna a Geba ta Benyamin. Sa’an nan Filistiyawa suka yi sansani a Mikmash. 17 Rundunar mayaƙa uku suka fito daga sansani Filistiyawa. Ɗaya ta nufi Ofra, zuwa ƙasar Shuwal. 18 Runduna guda kuma ta nufi Bet-Horon, ɗayan kuwa ta nufi iyakar da take fuskantar Kwarin Ziboyim wajen jeji.
19 Ba a sami maƙeri ɗaya a dukan ƙasar Isra’ila ba domin Filistiyawa sun ce, “In ba haka ba Ibraniyawa za su ƙera wa kansu takuba ko māsu.” 20 Saboda haka dukan Isra’ila sukan gangara zuwa wajen Filistiyawa domin su gyara bakin garemaninsu, da fartanansu, da gaturansu, da kuma laujunansu. 21 Duk lokacin da za su gyara bakin garmansu da fartanyarsu sai sun biya tsabar azurfa* biyu. Haka ma idan za su gyara gatari ko bakunan abin korar shanun noma sai sun biya tsabar azurfa ɗaya.
22 A ranar da yaƙi ya tashi, ba a sami wanda yake da takobi ko māshi ba a cikin mutanen da suke tare da Shawulu da Yonatan. Sai dai Shawulu da ɗansa Yonatan kaɗai.
Yonatan ya kai wa Filistiyawa hari
23 Ana nan sai sojojin Filistiyawa suka fita zuwa mashigin Mikmash.
* 13:21 tsabar azurfa. Da Ibraniyanci an rubuta biyu bisa uku na Shekel ne a nan. A zamaninsu wannan kuɗi ne mai yawa.