15
1 Yanzu ina tunashshe ku 'yan'uwa, game da bisharar nan da nake shelarwa, wadda kuka karba kuke kuma dogara da ita.
2 Da wannan bishara aka yi maku ceto, idan kuka rike wa'azi da na yi maku da karfi, sai in dama kun gaskanta a banza.
3 Domin na baku muhimmin sako kamar na farko da na karba: cewa Almasihu ya mutu domin zunubanmu, bisa ga nassosi,
4 cewa kuma an bizne shi, ya kuwa tashi daga matattu a rana ta uku bisa ga nassosi.
5 Cewa kuma ya bayyana ga Kefas, sa'an nan ga sha biyun.
6 Daga nan ya bayyana ga 'yan'uwa sama da dari biyar a lokaci guda. Wadanda mafi yawan su na da rai har yau, amma wasun su sun yi barci.
7 Daga nan ya bayyana ga Yakubu, da kuma ga manzannin duka.
8 A karshe, sai ya bayyana a gare ni, kamar dan da aka haifa bakwaini.
9 Gama ni ne mafi kankanta a cikin manzanni. Ban cancanci a kira ni manzo ba, domin na tsanantawa ikklisiyar Allah.
10 Amma saboda alherin Ubangiji ina matsayin da nake a yau, kuma alherin sa da ke ciki na ba a banza yake ba. A maimako, nayi aiki tukuru fiye da su duka. Amma duk da haka ba ni bane, amma alherin Allah da ke tare da ni.
11 Saboda haka ko nine ko Su, haka mukayi wa'azin, haka kuma kuka gaskata.
12 To idan anyi shela a matsayin cewa Yesu ya tashi daga matattu, tayaya wadansunku su ke cewa babu tashin matattu?
13 Amma idan babu tashin matattu, Almasihu ma ai ba a tashe shi ba kenan.
14 idan kuwa ba a tashi Almasihu ba, wa'azin mu ya zama banza kenan, haka kuma bangaskiyar ku ta zama banza.
15 Mun kuma zama shaidun karya game Allah kenan, muna shaida akan Allah cewa ya tashi Almasihu daga matattu alhali ko bai tashe shi ba.
16 Domin idan babu tashin matattu, kai, ko Almasihu ma ba a tashe shi ba kenan.
17 Idan har ba a tashi Almasihu ba, bangaskiyar ku a banza take, har yanzu kuma, kuna cikin zunuban ku.
18 To wadanda suka mutu cikin Almasihu kuma sun hallaka kenan,
19 idan a wannan rayuwa ce kadai muke da bege cikin Almasihu, to cikin dukkan mutane munfi kowa zama abin tausayi.
20 Amma yanzu, Almasihu ya tashi daga matattu, wanda ya sa shi ya zama nunar fari cikin tashi daga matattu.
21 Domin yadda mutuwa ta shigo duniya ta hanyar mutum guda, hakkan nan ma tashi daga matattu.
22 Gama kamar yadda a cikin Adamu duka suka mutu, haka kuma a cikin Almasihu za a rayar da duka.
23 Amma kowanne da tsarinsa: Almasihu, nunan fari, sannan su wadanda ke na Almasihu za a rayar da su lokacin zuwansa.
24 Sa'an nan karshen zai gabato, lokacin da Almasihu zai mika mulkin ga Allah Uba. sa'an nan ne zaya kawar da dukkan mulki, martaba da iko.
25 Gama mulkinsa zai habaka har sai ya sa dukkan makiyansa a karkashin sawayen sa.
26 Mutuwa kuwa, ita ce makiyi na karshe da za'a hallaka.
27 Domin “ yasa dukkan komai a karkashin ikonsa,” Amma da aka ce” yasa dukkan komai a karkashin ikonsa,” a sarari yake cewa wannan baya hada da wanda yasa dukan komai a karkashin ikonsa ba.
28 Idan dukan abu na karkashin mulkinsa, to Dan da kansa zaya kasance a karkashin ikon shi wanda yasa komai a karkashin ikonsa. Wannan zaya kasance ne saboda Allah Uba ya zama dukkan komai cikin dukkan komai.
29 ko kuma me zai faru da wadanda ake yi wa baftisma domin matattu? Idan kuwa babu tashin matattu sam sam, ina amfanin yi masu baftisma domin su?
30 Kuma me yasa muke cikin hadari kowace sa'a?
31 Ina mutuwa kullum. Wannan nake furtawa ta wurin fahariya, 'yan'uwa, wadda nake da ita cikin Almasihu Yesu Ubangijinmu.
32 Menene ribata, a idanun mutane, idan nayi kokowa da bisashe a Afisa, idan babu tashin matattu? “ bari mu ci mu sha, domin gobe zamu mutu.”
33 Kada fa a yaudare ku, domin “ tarayya da mugaye takan bata halayen kirki.”
34 “Ku natsu! kuyi zaman adalci! kada ku cigaba da zunubi. Domin wasunku basu da sanin Allah. Ina fadar wannan domin in baku kunya.
35 Amma wani zaya ce, “Yaya za'a yi tashin matattu? Wane irin jiki kuma zasu tashi da shi?
36 Ku jahilai ne sosai! Abinda ka shuka ba zaya fara girma ba sai ya mutu.
37 Abinda ka shuka ba jikin da zaya kasance bane, amma kwayar irin ne kawai. Wanda zaya zama alkama ko wani abu daban.
38 Amma Allah zaya bashi jiki yadda ya zaba, ga kowane kwayar iri da nashi jikin.
39 Ba duka jiki ne yake iri daya ba. A maimako, akwai jiki irin na mutane, akwai kuma wani irin na dabbobi, kuma wani jikin irin na tsuntsaye, kuma da irin na kifi.
40 Akwai kuma jikina na samaniya da jikina na duniya. Amma daukakar jikin samaniya wata daban ce kuma daukakar jikin duniya daban ce.
41 Akwai daukaka irin ta rana, da kuma wata daukakar irin ta wata, da kuma wata daukakar irin ta taurari. Domin wani tauraron ya bambanta da wani wajen daukaka.
42 Haka yake a tashin matattu. Abinda aka shuka mai lalacewa ne, wanda aka tayar marar lalacewa ne.
43 An shuka shi cikin rashin daraja; an tayar da shi cikin daukaka. An shuka shi cikin rauni; an tayar da shi cikin iko.
44 An shuka shi jiki na zahiri; an tayar da shi jiki na ruhaniya. Idan akwai jiki na zahiri, to akwai jiki na ruhaniya.
45 Haka kuma aka rubuta, “ Adamu na farko ya zama rayayyen taliki.” Adamu na karshe ya zama Ruhu mai bayar da rai.
46 Amma na ruhaniyar ba shine ya fara zuwa ba amma na zahirin, daga nan na ruhaniyar.
47 Mutumin farkon ai daga turbaya ya fito, wato na duniya. Amma shi na biyun daga sama yake.
48 kamar yadda mutumin ya fito daga turbaya haka ma wadanda aka halitta da turbaya. kamar yadda mutumin yake daga sama haka ma wadanda ke na sama.
49 Kamar yadda muke dauke da jiki mai kamannin turbaya, haka ma zamu kasance da kamannin mutumin sama.
50 To wannan na fada, 'yan'uwa, cewa nama da jini ba za su gaji mulkin Allah ba. Haka kuma mai lalacewa ba za ya gaji marar lalacewa ba.
51 Duba! ina gaya maku asirtacciyar gaskiya: Ba dukanmu zamu mutu ba, amma dukanmu za a canza mu.
52 Za a canza mu nan da nan, cikin keftawar ido, a kaho na karshe. Domin za a busa kaho, kuma za a tada matattu marasa lalacewa, kuma za a canza mu.
53 Domin wannan jiki mai lalacewa dole ya sanya jiki marar lalacewa, kuma wannan jiki mai mutuwa dole ya sanya marar mutuwa.
54 Amma idan wannan jiki mai lalacewa ya sanya marar lalacewa, kuma wannan jiki mai mutuwa ya sanya marar mutuwa, sai abinda aka rubuta ya cika, “An hadiye mutuwa cikin nasara.”
55 “Mutuwa, ina nasararki? Mutuwa, ina dafinki?”
56 Gama dafin mutuwa zunubi ne, kuma ikon zunubi shari'a ce.
57 Amma godiya ga Allah, wanda ya bamu nasara ta wurin Ubangijinmu Yesu Almasihu!
58 Saboda haka, ya ku 'yan'uwana kaunatattu, ku dage kuma kada ku jijjigu. Ko yaushe ku habaka da aikin Ubangiji, domin kun san cewa aikinku cikin Ubangiji ba a banza yake ba.