16
Yanzu game da zancen tattara gudunmuwa ga masu bi, kamar yadda na umurci ikilisiyun Galatiya, haka za ku yi. A ranar farko ga mako, kowannen ku ya ajiye wani abu, yana tarawa bisa ga iyawarku. Ku yi haka don in na zo ba sai an tattara ba. Sa'adda na zo, zan aiki duk wadanda kuka yarda da su da wasiku don su kai sakonku Urushalima. Sannan idan ya dace nima in tafi, sai su tafi tare da ni. Zan zo wurinku sa'adda na ratsa Makidoniya. Domin zan ratsa ta makidoniya. Meyuwa in jima a wurinku, har ma in yi damuna, domin ku taimaka mani game da tafiyata, duk inda za ni. Gama ba na so in yi maku gani na gajeren lokaci. Don ina so in dau lokaci tare da ku, idan Ubangiji ya yarda. Amma zan tsaya Afisus har ranar Fentikos. Gama an bude mani kofa mai fadi, kuma akwai magabta da yawa. 10 Sa'adda Timoti ya zo, ku tabbata ya sami sakewa acikinku, tun da aikin Ubangiji yake yi kamar yadda nake yi. 11 Kada fa kowa ya rena shi. Ku tabbata kun sallame shi lafiya, domin ya komo gare ni, don ina duban hanyarsa tare da yan'uwa. 12 Game da zancen dan'uwanmu Afollos kuwa, na karfafa shi ya ziyarce ku tare da 'yan'uwa. Sai dai baya sha'awar zuwa yanzu. Amma zai zo sa'adda lokaci ya yi. 13 Ku zauna a fadake, ku tsaya daram cikin bangaskiya, kuna nuna halin maza, ku yi karfin hali. 14 Bari dukan abinda kuke yi ayi shi cikin kauna. 15 Kun dai sani iyalin gidan Sitefanas su suka fara tuba a Akaya, kuma sun bada kansu ga yi wa masu bi hidima. Yanzu ina rokonku, 'yan'uwa, 16 kuyi biyayya da irin wadannan mutane da duk wanda ke taimakawa a cikin aikin, yana kuma fama tare da mu. 17 Na yi farinciki da zuwan Sitefanas, da Fartunatas, da Akaikas. Sun debe mini kewarku. 18 Gama sun wartsakar da ruhuna da naku kuma. Don haka, Sai ku kula da irin wadannan mutane. 19 Ikilisiyoyin kasar Asiya suna gaishe ku. Akila da Bilkisu, tare da ikilisiyar da take taruwa a gidansu, suna gaishe ku cikin Ubangiji. 20 Dukan 'yan'uwa masu bi na gaishe ku. Ku gaida juna da sumba maitsarki. 21 Ni Bulus, nake rubuta wannnan da hannuna. 22 Duk wanda ba ya kaunar Ubangiji bari ya zama la'ananne. Ubangijinmu, Ka zo! 23 Alherin Ubangiji Yesu ya kasance tare da ku. 24 Bari kaunata ta kasance tare da ku duka a cikin Almasihu Yesu. [ Amin ].