11
1 To wani mutum mai suna Li'azaru, yayi rashin lafiya. Shi mutumin Baitanya ne, wato kauyen su Maryamu da 'yar'uwarta Matta.
2 Wato wannan Maryamu da ta shafe Ubangiji da mur ta kuma share masa kafafunsa da gashin kanta, wadda dan'uwanta Li'azaru ke rashin lafiya.
3 'Yan'uwannan mata suka aika sako wurin yesu, cewa, “Ubangiji, duba, shi wanda kake kauna yana rashin lafiya”.
4 Da Yesu ya ji, sai ya ce “Wannan ciwo ba zai kai ga mutuwa ba, amma domin daukakar Allah ne, domin Dan Allah ya sami daukaka tawurin ta”.
5 Yesu yana kaunar Matta, da 'yar'uwarta da Li'azaru.
6 Da yaji cewa Li'azaru na rashin lafiya, sai ya tsaya kwana biyu a inda ya ke.
7 Bayan haka, sai ya ce wa almajiransa, “Bari mu je Yahudiya kuma.”
8 Sai almajiransa suka ce masa, “Mallam, harwayau Yahudaya na neman ka domin su jefe ka da duwatsu, kuma kana son komawa can?”
9 Yesu ya amsa, “Ba sa'a goma sha biyu ce ta haske a rana guda ba? Idan mutum ya yi tafiya da rana, ba za ya yi tuntube ba, domin yana gani ta wurin hasken wannan duniya.
10 Amma idan mutum ya yi tafiya chikin dare, za ya yi tuntube domin haske ba ya tare da shi.
11 Ya fadi wadannan al'amura, kuma bayan wadannan abubuwa, sai ya ce masu, “Abokinmu Li'azaru ya yi barci, amma zan je don In tashe shi daga barci”.
12 Sai almajirai suka ce masa, “Ubangiji, idan barci yake yi, ai za ya farka.”
13 Yesu kuwa ya yi maganar mutuwar Li'azaru ne, amma su suna tsammani yana magana akan barci ne na hutu.
14 Sai Yesu ya yi masu bayani cewa, “Li'azaru ya mutu.
15 Ina farinchiki domin ku, da bani a wurin domin ku gaskata. Bari mu je wurinsa.”
16 Toma wanda ake kira Dan tagwaye, ya ce wa sauran almajirai, “Bari mu tafi domin mu mutu tare da Yesu.”
17 Da Yesu ya iso, sai ya tarar cewa Li'azaru ya rigaya ya yi kwana hudu a kabari.
18 Baitanya kuma tana kusa da Urushalima, 'yar tafiya marar nisa ce a tsakanin su.
19 Yahudawa dayawa sun zo wurin Maryamu da Matta domin su yi masu ta'aziyar mutuwar dan'uwansu.
20 Da Matta ta ji cewa Yesu na zuwa, sai ta tafi domin ta same shi, amma Maryamu na zamne a cikin gida.
21 Matta ta ce wa Yesu, “Ubangiji, da kana nan tare da mu, da dan'uwana baya mutu ba”.
22 Ko yanzu na san cewa duk abinda ka roka a wurin Allah, za ya ba ka.
23 Yesu ya ce mata, “Dan'uwanki za ya rayu kuma.
24 Sai Matta ta ce masa, “Na san zaya rayu kuma a tashin mattatu na ranar karshe.”
25 Yesu ya ce mata, “Ni ne tashin matattu, ni ne kuma rai; wanda ya bada gaskiya gare ni, ko ya mutu, za ya rayu;
26 Kuma duk wanda yake raye, ya kuma bada gaskiya gare ni, ba zai mutu ba dadai. Kin gaskata da wannan?”
27 Sai ta ce masa, “I, Ubangiji, Na gaskata cewa kaine Almasihu, Dan Allah, wanda ke zuwa duniya.
28 Sa'adda ta fadi haka, sai ta koma ta kira yar'uwarta Maryamu gefe guda. Ta ce, “mallam ya iso, kuma yana kiran ki.”
29 Da ta ji haka, sai ta tashi da sauri ta tafi wurin sa.
30 Yesu bai rigaya ya shiga kauyen ba, yana nan inda Matta ta zo ta same shi.
31 Da Yahudawan nan dake tare da Maryamu, wato wadannan da suka zo mata ta'aziya, suka ga ta fita daga chikin gida da sauri, sai suka bi ta, suna tsammanin cewa ta tafi ta yi kuka ne a kabari.
32 Da Maryamu ta kai inda Yesu ya ke, sai ta fadi gaban sawayensa, ta ce, “Ubangiji, inda kana tare da mu, da dan'uwana bai mutu ba”.
33 Da Yesu ya gan ta tana kuka, da wadannan Yahudawa da suka bi ta, sai ya yi juyayi a ruhu ya damu kuma;
34 sai ya ce, “A ina kuka kwantar da shi?” Sai suka ce masa, “Ubangiji, zo ka gani.”
35 Yesu ya yi kuka.
36 Sai Yahudawa suka ce, “Dubi yadda yake kaunar Li'azaru!”
37 Amma wadansun su suka ce, “Shi wannan mutum da ya iya ba makaho ganin gari, da bai iya hana wannan mutum mutuwa ba?
38 Yesu yana cikin juyayi kuma a cikin kansa, sai ya tafi kabarin. Kabarin a kogo ne an kuma rufe bakinsa da dutse.
39 Sai Yesu ya ce, “A kawar da dutsen.” Matta yar'uwar Li'azaru wanda ya mutu, ta ce wa Yesu, “Ubangiji, Yanzu jikin ya ruba domin ya kai kwana hudu da mutuwa”.
40 Yesu ya ce mata, “Ba na ce maki idan kin gaskata za ki ga daukakar Allah ba?”
41 Sai suka kawar da dutsen. Yesu ya daga idanunsa ya ce, “Uba, na gode maka domin kana ji na.”
42 Na san kana ji na a kowane lokaci, amma domin wannan taro da ke tsaye kewaye da ni nike wannan magana, domin su bada gaskiya cewa kaine ka aiko ni.”
43 Bayan ya yi wannan magana, sai ya daga murya ya ce, “Li'azaru, ka fito!”
44 Sai mataccen ya fito; kafafunsa da hannayensa na daure da likkafani, fuskarsa kuma na lullube da tsumma. Yesu ya ce masu, “Ku kwance shi, ya tafi”.
45 To dayawa daga cikin yahudawan da suka zo wurin Maryamu suka kuma ga abinda Yesu ya yi, suka gaskata da shi;
46 amma wadansu suka koma wurin farisawa suka fada masu abubuwan da Yesu ya yi.
47 Sai manyan firistoci da farisawa suka tara majalisa wuri guda, suka ce, “menene za mu yi?” Mutumin nan yana alamu masu yawa.
48 Idan mun kyale shi haka, duka za su gaskata da shi; Romawa za su zo su kwace wurinmu da al'ummar mu.
49 Duk da haka, wani daga cikin su wato, Kayafas wanda shine babban firist a wannan shekara, ya ce da su, “baku san komai ba”.
50 Ba ku lura cewa ya fi maku kyau mutum daya ya mutu domin mutane, a maimakon dukan al'umma ta hallaka.”
51 Ya fadi wannan ne ba don kansa ba, amma sabo da shine babban firist, ya yi anabci ne cewa ya kamata Yesu ya mutu domin al'ummar;
52 kuma ba don alummar kawai ba, amma domin a tattara 'ya'yan Allah da suke warwatse ko'ina wuri daya.
53 Tun daga wannan rana suka fara neman hanyar da za su kashe Yesu.
54 Tun daga nan Yesu ya dena tafiya a sarari chikin Yahudawa, amma sai ya koma wani yanki kusa da jeji a wani gari da ake kira Ifraimu. A can kuma ya zamna da almajiransa.
55 Idin ketarewa na Yahudawa ya yi kusa, da yawa sun tafi Urushalima daga yankin kasar kamin ranar idi domin su tsarkake kan su.
56 Suka shiga neman Yesu, suna magana da junan su yayin da suke tsaitsaye a haikali, cewa “me kuke tunani? Ba za ya zo idin bane?”
57 Babban firist da farisawa sun rigaya sun ba da umurni cewa duk inda aka ga Yesu a zo a shaida domin su kama shi.