12
1 Kwana shidda kafin idin ketarewa, Yesu ya zo Baitanya inda Li'azaru yake, wato wannan da Yesu ya tada daga matattu.
2 Sai suka shirya masa abinci a wurin kuma Matta ce ke hidima, Li'azaru kuwa ya kasance cikin wadanda ke kan tebiri tare da Yesu.
3 Sai Maryamu ta dauki wani turare da aka yi da man nard, ta shafe kafafun Yesu da shi, ta kuma share kafafun nasa da gashin kanta. Sai gida ya cika da kamshin turaren.
4 Yahuza Iskariyoti, daya daga cikin almajiransa, wanda zai bashe shi, ya ce, “
5 “Me yasa ba a sayar da wannan turare dinari dari uku a ba gajiyayyu ba?”
6 Ya fadi haka ba don ya damu da gajiyayyu ba, amma domin shi barawo ne: shi ne ma'aji, kuma yana sata daga jakkar kudi.
7 Yesu ya ce, “Ku kyale ta ta ajiye abinda ta tanada domin jana'iza ta.
8 Gajiyayyu suna tare da ku a koyaushe, ni kuwa ba zan kasance da ku koyaushe ba.
9 To babban taron Yahudawa sun ji cewa Yesu yana wurin, sai suka zo, ba don Yesu kawai ba amma domin su ga Li'azaru, wanda Yesu ya tada daga matattu.
10 Sai manyan firistoci suka kulla makirci akan yadda za su kashe Li'azaru shima;
11 domin saboda shi ne yahudawa dayawa suka je suka bada gaskiya ga Yesu.
12 Kashegari, babban taro suka zo idin. Da suka ji cewa Yesu na zuwa Urushalima,
13 Sai suka dauki ganyen dabino suka fita gari suka tare shi da kira mai karfi suna cewa, “Hosanna! Mai albarka ne wanda yake zuwa cikin sunan Ubangiji, Sarkin Isra'ila.
14 Yesu ya sami wani Aholakin jaki, ya hau kansa; kamar yadda aka rubuta,
15 “Kada ki ji tsoro ke 'yar Sihiyona; duba, ga Sarkinki na zuwa, zaune a kan danJaki”.
16 Almajiransa basu fahimci wannan al'amari ba da farko, amma bayan da aka daukaka Yesu, sai suka tuna cewa an rubuta wadannan abubuwa game da shi, kuma sun yi masa wadannan abubuwa.
17 Sai taron da ke tare da Yesu a ranar da ya kira Li'azaru daga kabari ya kuma tashe shi daga matattu, suka bada shaida.
18 Domin wannan ne kuma taron suka zo domin su sadu da shi saboda sun ji cewa ya yi wannan alama.
19 Don haka, sai farisawa suka shiga magana a tsakanin su suna cewa “Duba, babu abinda zaku iya yi; kun ga, duniya ta gama bin sa.
20 Akwai wadansu Helinawa cikin wadanda suka je sujada a idin.
21 Wadannan suka tafi wurin filibus, mutumin Betsaida da ke Galili, suka ce masa, “Mallam, muna so mu ga Yesu.
22 Filibus ya tafi ya fadawa Andrawus; sai Andrawus ya tafi tare da Filibus, suka kuwa gaya wa Yesu.
23 Yesu ya amsa masu ya ce, “sa'a ta zo da za'a daukaka Dan mutum.
24 Hakika, hakika, Ina ce maku, in ba kwayar alkama ta fadi kasa ba ta mutu, za ta kasance ita kadai; amma idan ta mutu, za ta bada 'ya'ya masu yawa.
25 Duk wanda yake son ransa, zai rasa shi; amma wanda ba ya son ransa a duniyan nan za ya kiyaye shi domin rayuwa ta har abada.
26 Idan wani na bauta mani, to bari ya biyo ni; kuma duk inda nike, a can bawana zai kasance kuma. Duk wanda ke bauta mani, Uban zai girmama shi.
27 Yanzu raina na cikin damuwa, to me zan ce? 'Uba, ka cece ni daga wannan sa'a? Amma Saboda wannan dalili ne na zo wannan sa'a.
28 Uba, ka daukaka sunanka”. Sai wata murya daga sama ta ce, “Na daukaka shi, zan kuma sake daukaka shi.
29 Daganan sai taron dake tsaye kuma suka ji muryar, suka ce an yi tsawa. Wasu suka ce, “Mala'ika ya yi magana da shi”.
30 Yesu ya amsa ya ce, “wannnan murya ta zo ba saboda ni ba, amma domin ku.”
31 Yanzu za'a shar'anta duniya. Yanzu za'a kori mai mulkin duniyan nan.
32 Sa, annan ni, idan an daga ni daga duniya, zan jawo dukan mutane zuwa gare ni”.
33 Ya fadi wannan ne domin ya nuna irin mutuwar da za ya yi.
34 Taro suka amsa masa cewa, “Mun ji a cikin shari'a cewa Almasihu za ya kasance har abada. Yaya za ka ce, 'za'a daga dan mutum'? Wanene wannan dan mutum?”
35 Yesu ya ce masu, “Nan da lokaci kadan za ku kasance da haske, ku yi tafiya tun haske na tare da ku, kada duhu ya mamaye ku. Wanda ke tafiya cikin duhu, bai san inda za shi ba.
36 Ku gaskata ga haske tun yana tare da ku domin ku zama yayan haske”. Yesu ya fadi wadannan abubuwa sannan ya tafi ya boye masu.
37 Kodashike Yesu ya yi alamu da dama a gabansu, duk da haka ba su gaskata shi ba.
38 Saboda maganar annabi Ishaya ta cika, wadda ya ce, “ Ubangiji, wa ya gaskata rahoton mu? Ga wa kuma hannun Ubangiji ya bayyana?
39 Saboda wannan dalili basu gaskata ba, gama Ishaya ya sake cewa,
40 ya makantar da su, ya kuma taurare zuciyarsu, saboda kada su gani da idanunsu, su kuma sami fahimta da zuciyarsu, su juyo wurina in warkar da su.
41 Ishaya ya fadi wadannan abubuwa ne domin ya hangi daukakar Yesu ya kuma yi magana game da shi.
42 Amma duk da haka, dayawa cikin shugabanni suka gaskata Yesu. Amma saboda farisawa, basu shaida shi a sarari ba, domin kada a kore su daga majami'a.
43 Suna son yabo daga mutane fiye da yabon dake zuwa daga Allah.
44 Yesu ya yi magana da babbar murya, ya ce, “Wanda ya gaskata ni, ba ni yake gaskatawa kadai ba, amma kuma yana gaskata wanda ya aiko ni,
45 kuma wanda ke gani na, yana ganin shi wanda ya aiko ni.
46 Na zo ne a matsayin haske a duniya, saboda duk wanda ya gaskata da ni ba za ya yi tafiya cikin duhu ba.
47 Duk wanda ya ji maganata baya gaskata ba, ba ni hukunta shi; gama ban zo in yi wa duniya hukunci ba, amma don in ceci duniya.
48 Wanda ya ki ni, ya kuma ki ya karbi magana ta, akwai wanda za ya yi masa hukunci. Kalmar da na fada, ita ce za ta yi masa hukunci a rana ta karshe.
49 Maganar da ni ke yi, ba ra'ayina ba ne. Amma Uba wanda ya aiko ni shi ke bani umarni game da abin da zan ce da abin da zan fadi.
50 Na san umarninsa rai ne madawwami, don haka na ce - kamar yadda Uba ya fada, haka ni ma nake fadi.”