12
A wannan lokaci, Yesu ya tafi a ranar Asabaci, ya bi cikin gonar hatsi. Almajiransa na jin yunwa, sai suka fara zagar hatsi suna ci. Amma da Farisawa suka gan su, sai su ka ce wa Yesu. “Duba, almajiranka su na yin abin da doka ta haramta a ranar Asabaci.” Amma Yesu ya ce masu, “Baku karanta abin da Dauda ya yi ba, lokacin da ya ke jin yunwa, tare da mazan da ke tare da shi? Yadda ya shiga gidan Allah, ya ci gurasar alfarwa da doka ta hana shi ko mazan da ke tare da shi su ci, sai dai Firistoci ne kawai doka ta basu damar ci? Sa'annan ba ku karanta cikin shari'a cewa, a ranar Asabaci, Firistoci da ke cikin haikali na sabawa ranar Asabaci, amma kamar ba su yi laifi ba? Amma ina tabbatar maku da cewa, wani wanda ya fi haikali girma yana nan. In da kun san ma'anar wannan 'Na fi son jinkai fiye da hadaya,' da baku shari'anta wa marar laifi ba. Gama Dan mutum shine Ubangijin Asabaci.” Sa'annan Yesu ya bar wannan wuri, ya shiga majami'ar su. 10 Sai ga wani mutum wanda hannun sa ya shanye, sai Farisawa suka tambayi Yesu, cewa, “Doka ta halarta a yi warkarwa a ranar Asabaci?” Domin su zarge shi a kan zunubi. 11 Yesu ya ce masu, “Wanene a cikin ku, wanda idan ya na da tunkiya guda, sa'annan tunkiyar nan ta fada a rami mai zurfi a ranar Asabaci ba zai kamo ta ya fitar da ita ba? 12 Yaya za a kwatanta darajar mutum da tunkiya! Saboda haka ya halarta a yi alheri ranar Asabaci.” 13 Sai Yesu ya ce wa mutumin nan “Mika hannun ka.” Ya mike hannunsa, sai hannun nan ya dawo lafiyaye kamar dayan hannunsa. 14 Amma Farisawa su ka fita waje su ka fara mugun shiri domin sa. Su na neman hanyar da za su kashe shi. 15 Da Yesu ya fahimci wannan, sai ya janye kan sa daga nan. Mutane da dama su ka bi shi, ya warkar da su duka. 16 Ya dokace su da kada su bayyana shi ga kowa, 17 domin ya zama gaskiyar abin da aka fada ta wurin annabi Ishaya, cewa, 18 “Dubi, bawa na zababbe; kaunatacce na, wanda ya ke faranta mani raina sosai. Zan sa Ruhu na bisan sa, za ya furta hukunci zuwa al'ummai. 19 Ba za ya yi jayayya ko tada murya ba, babu wanda za ya ji muryar sa a karabku. 20 Ba zai karya kara da ya tankwashe ba; ba zai kashe fitilar da ta kusa mutuwa ba; sai ya kawo hukunci ga nasara. 21 Sa'annan al'ummai za su dogara a ga sunansa. 22 Sa'annan wani mutum, makaho ne, kurma kuma, aljannu kuma na cikinsa, an kawo shi wurin Yesu. Ya warkar da shi, ya sami ganin gari ya kuma yi magana. 23 Jama'a su ka yi mamaki kwarai, su na cewa, “Ko wannan ne Dan Dawuda?” 24 Amma da Farisawa su ka ji wannan al'ajibi, sai su ka ce, “Mutumin nan yana fitar da aljannu ta wurin Bahalzabuba sarkin aljannu ne.” 25 Amma Yesu ya san tunanin su, sai ya ce. “Duk mulkin da ya rabu gaba da kan sa, ba zaya tsaya ba, duk wani birni da ya rabu ba zai tsaya ba, ko gida da ya tsage, za ya rushe. 26 Idan Shaidan ya fitar da Shaidan, ya rabu gaba da kansa. Yaya mulkin sa za ya tsaya? 27 Idan Ina fitar da aljannu da ikon Ba'alzabuba, ta wurin wa masu bin ku su ke fitar da su? Saboda haka, su za su shari'anta ku. 28 Amma idan ina fitar da aljannu da Ruhun Allah ne, hakika mulkin Allah ya zo gare ku. 29 Kuma ta yaya mutum za ya shiga gidan mai karfi ya kwashe masa kaya ba tare da ya fara daure shi ba? Sa'annan ne za ya iya satar masa kaya daga gidansa. 30 Wanda baya tare da ni yana gaba da ni ke nan, wanda kuma baya tarawa tare da ni, yana watsarwa ne. 31 Saboda haka ina ce maku, kowanne zunubi da sabo, za a gafarta wa mutum, amma sabon Ruhu Mai Tsarki, ba za a gafarta shi ba. 32 Duk wanda yayi batanci ga Dan Mutum, za a gafarta masa. Amma duk wanda yayi batanci game da Ruhu Mai Tsarki ba za a gafarta masa ba, a nan duniya da har abada. 33 Ko dai a mai da itace mai kyau 'ya'yansa kuma su yi kyau, ko a mai da itace marar kyau 'ya'yansa kuma marasa kyau, gama ana sanin itace ta wurin 'ya'yansa. 34 Ku 'ya'yan macizai, tun da ku miyagu ne, yaya za ku iya fadin abubuwa nagari? Gama daga cikar zuciya baki ke magana. 35 Mutumin kirki daga ajiyar zuciyarsa ya kan fitar da abubuwa masu kyau, mugun mutum kuma daga mummunar ajiyar zuciyarsa ya kan fitar da abubuwan mugunta. 36 Sa'annan ina ce maku a ranar shari'a, mutane za su bada lissafin abubuwan banza da su ka fadi. 37 Gama ta wurin maganganun ku, za a 'yantar da ku, ta wurin maganganun ku kuma za a kashe ku.” 38 Sa'annan wadansu Malaman Attaura, da Farisawa suka amsa suka ce wa Yesu, “Mallam, muna so mu ga wata alama daga gare ka.” 39 Amma Yesu ya amsa ya ce masu, “Mugun zamani da mazinaciyar tsara, su na bukutar alama. Amma babu alamar da za a ba su, sai dai alamar annabi Yunusa. 40 Gama yadda Yunusa ya yi kwana uku da dare uku a cikin babban kifi, haka ma Dan Mutum zaya yi kwana uku da dare uku a cikin zuciyar kasa. 41 Mutanen Nineba za su tsaya a ranar shari'a da wannan zamani sannan su kashe su. Domin sun tuba da suka ji wa'azin Yunusa, amma duba wanda ya fi Yunusa yana nan. 42 Sarauniyar Kudu za ta tashi da mutanen wannan zamani ta kuma kashe su. Ta zo daga karshen duniya domin ta ji hikimar Sulaimanu, kuma duba, wanda ya fi Sulaimanu yana nan. 43 Idan kazamin ruhu ya rabu da mutum, ya kan wuce ya nemi wuraren da ruwa yake domin ya huta, amma bai samu ba. 44 Sai ya ce, 'zan koma gidana inda na fito'. Bayan ya dawo, sai ya tarar da gidan nan an share shi ya zama da tsabta. 45 Sai ya koma ya kawo wadansu ruhohi guda bakwai, wadanda su ka fi shi mugunta, sa'annan dukan su su zo su zauna a nan. Sa'annan yanayin mutumin nan na karshe ya fi na farko muni. Haka zaya kasance ga wannan mugun zamani. 46 Sa'adda Yesu ya ke yi wa Jama'a jawabi, sai mahaifiyarsa da 'yan'uwansa su ka zo su ka tsaya a waje, suna neman su yi magana da shi. 47 Sai wani ya ce masa, “Duba, mahaifiyarka da 'yan'uwanka suna tsaye a waje, suna so su yi magana da kai”. 48 Amma Yesu ya amsa ya ce wa shi wanda ya gaya masa, “Wacece mahaifiyata? Kuma su wanene 'yan'uwana?” 49 Sai ya mika hannu ya nuna almajiransa ya ce, “Duba, ga mahaifiyata da 'yan'uwana! 50 Gama duk wanda yake aikata nufin Ubana wanda ya ke cikin sama, shine dan'uwana, da 'yar'uwata da mahaifiyata.”