13
A waccan rana Yesu ya fito daga gida ya zauna a gefen teku. Taro mai yawan gaske kuwa suka kewaye shi, sai ya shiga cikin kwalekwale ya zauna. Dukan taron kuwa na tsaye a bakin tekun. Sai Yesu ya fada masu abubuwa da yawa cikin misalai. Ya ce, “Wani mai shuka, ya tafi yayi shuka. Da yayi shukar, wadansu irin suka fadi a kan hanya, sai tsunsaye suka zo suka cinye su. Wadansu irin kuwa suka fadi a kan duwatsu, wurin da babu kasa. Nan da nan sai suka tsira, domin kasar babu zurfi. Amma da rana ta taso, sai suka yankwane domin ba su yi saiwa ba, suka kuwa bushe suka zube. Wasu irin kuwa suka fada a cikin kayayuwa. Kayayuwan kuwa suka shake su. Wasu irin kuwa suka fada a wuri mai kyau suka ba da tsaba, wani ya ba da dari, wasu sitin, wasu kuma talatin. Duk mai kunnen ji, bari ya ji. 10 Almajiran suka zo suka ce ma Yesu, “Don me ka ke yi wa taron magana da misali?” 11 Yesu ya amsa ya ce masu, “An baku 'yanci ku fahimci asiran mulkin sama, amma gare su ba a bayar ba. 12 Domin wanda yake da shi, za a kara masa, zai kuma samu dayawan gaske. Amma duk wanda ba shi da shi, sai a dauke har ma abin da yake dashi. 13 Saboda haka na yi masu magana cikin misalai, amma ko da ya ke sun gani, duk da haka ba su gani ba. Kuma ko da yake sun ji, hakika ba su ji ba, balle ma su fahimta. 14 A gare su ne annabcin Ishaya ya cika, wanda yake cewa, “Game da sauraro zaku saurara, amma ba za ku fahimta ba. Game da gani kuma za ku kalla, amma ba za ku gane ba. 15 Domin zuciyar mutanen nan ta duhunta, sun taurare ga saurare, kuma sun rufe idanunsu domin kada su gani da idanunsu, ko kuwa su ji da kunnuwansu, ko kuwa su fahimta da zukatansu, saboda su juyo kuma in warkar da su'. 16 Amma idanunku masu albarka ne, domin sun gani, haka ma kunnuwanku, domin sun ji. 17 Hakika ina gaya muku, annabawa da mutane dayawa masu aldalci sun yi marmarin ganin abin da kuka gani, amma ba su sami ganin su ba. Sun yi marmarin jin abin da kuka ji, ba su kuwa ji su ba. 18 Ku saurari misalin nan na mai shuka. 19 Idan wani ya ji maganar mulkin sama amma bai fahimce ta ba, sai mugun nan ya zo ya kwace abinda aka shuka a zuciyarsa. Wannan shine irin da aka shuka a kan hanya. 20 Shi wanda aka shuka akan duwatsu, shine wanda ya ji maganar ya kuma karbe ta da murna nan da nan. 21 Duk da haka, bai yi karfi cikin ta ba kuma nan ba da dadaiwa ba. Da wahala da tsanani suka taso saboda maganar, sai ya yi tuntube nan da nan. 22 Shi wanda aka shuka a cikin kayayuwa wannan shine wanda ya ji maganar, amma dawainiyar duniya da kuma yaudarar dukiya suka shake maganar, sai ya kasa ba da 'ya'ya. 23 Shi wanda aka shuka a kasa mai kyau, wannan shine wanda ya ji maganar, ya kuma fahimce ta. Wannan shine wanda ba da 'ya'ya da gaske; wadansu ribi dari, wadansu sittin, wasu kuma talatin.” 24 Yesu ya sake ba su wani misali, yana cewa “Za a kwatanta mulkin sama da wani mutum wanda ya shuka iri mai kyau a gona. 25 Amma da mutane suka yi barci, magabcin sa ya zo ya shuka ciyayi a cikin alkamar, ya kuwa yi tafiyarsa. 26 Sa'adda suka yi toho suka kuma ba da tsaba, sai ciyayin suka bayyana. 27 Bayin mai gonar kuwa suka zo suka ce masa, maigida, ashe ba iri mai kyau ka shuka a gonarka ba? ya ya aka yi ta kasance da ciyayi? 28 Ya ce masu, “Magabci ne ya yi wannan”. Sai bayin suka ce masa, 'kana so mu je mu tuge su ne?' 29 Mai gonar ya ce, 'A'a, kada a garin tuge ciyayin, ku tuge tare da alkamar. 30 Bari dukan su su girma tare har lokacin girbi, a lokacin girbin zan gaya wa masu girbin, “Ku tuge ciyayin da farko a daura su dami dami sai a kona su, amma a tara alkamar a kai rumbunana.'” 31 Sai Yesu ya sake yin magana da su cikin misalai, yana cewa “Za a kwatanta mulkin sama da kwayar mustad, wanda wani mutum ya shuka a lambunsa. 32 Wannan iri shine mafi kankanta cikin dukan iri. Amma bayan ya yi girma, sai ya fi dukan ganyaye dake lambun. Ya zama itace, har ma tsuntsayen sama su yi sheka a rassansa.” 33 Yesu ya sake fada masu wani misali. “Za a kwatanta mulkin sama da yisti da mace takan dauka ta kwaba gari da shi mudu uku har sai ya yi kumburi.” 34 Duk wadannan abubuwa Yesu ya fada wa taron cikin misalai. Babu abinda ya fada masu da ba a cikin misali ba. 35 Wannan ya kasance ne domin abinda annabin ya fada ya zama gaskiya, da ya ce, “Zan buda bakina da misali. In fadi abubuwan da ke boye tun daga halittar duniya.” 36 Sai Yesu ya bar taron ya shiga cikin gida. Amajiransa suka zo wurin sa suka ce, “Ka fasarta mana misalan nan a kan ciyayin da ke gonar” 37 Yesu ya amsa kuma ya ce, “Shi wanda ya shuka iri mai kyau Dan Mutum ne. 38 Gonar kuwa duniya ce; iri mai kyau kuma sune 'ya'yan mulkin. Ciyayin kuma sune 'ya'yan mugun, 39 magabcin da ya shuka su kuma shaidan ne. Girbin shine karshen duniya, kuma masu girbin sune mala'iku. 40 Saboda haka, kamar yadda aka tara ciyayin aka kona su da wuta, haka ma zai faru a karshen duniya. 41 Dan Mutum zai aiki mala'ikunsa, kuma su tara dukan abubuwan da ke sa zunubi daga cikin mulkinsa, da kuma wadanda su ka yi aikin mugunta. 42 Za su jefa su cikin korama ta wuta, inda za a yi kuka da cizon hakora. 43 Sa'an nan ne mutane masu adalci za su haskaka kamar rana a mulkin Ubansu. Bari mai kunnen ji, ya ji. 44 Mulkin sama kamar dukiya ce da ke boye a gona. Mutum ya samu sai ya boye ta, ya tafi cikin murna, ya sayar da mallakarsa kuma ya sayi filin. 45 Haka ma za a kwatanta mulkin sama da wani attajiri mai neman Lu'ulu'ai masu daraja. 46 Da ya sami lu'ulu'u daya mai darajar gaske, ya je ya sayar da dukan mallakarsa ya kuma saye shi. 47 Haka kuma, za a kwatanta mulkin sama da taru da aka jefa cikin teku, ya kuwa tara hallitu iri-iri. 48 Da ya cika, sai masuntan suka jawo shi bakin tekun. Sai suka zauna suka tara kyawawan abubuwan a taska, amma munanan abubuwan, suka watsar da su. 49 Haka zai kasance a karshen duniya. Mala'iku za su zo su ware miyagu daga cikin masu adalci. 50 Za su jefa su cikin korama ta wuta, inda za a yi kuka da cizon hakora. 51 Kun fahimci dukan wadannan abubuwa? Amajiran suka ce da shi, “I”. 52 Sai Yesu ya ce masu, “Saboda haka kowane malamin attaura da ya zama almajirin mulkin sama, yana kamar mutum mai gida wanda ya zaro tsoho da sobon abu daga taskarsa.” 53 Daga nan, sa'adda Yesu ya kammala ba da wadanan misalai, sai ya tafi ya bar wurin. 54 Sai Yesu ya shiga yankinsa ya koyar da mutane a masujadarsu. Saboda haka suka yi mamaki suna cewa, “Daga ina wannan mutumin ya sami hikimarsa da al'ajibai? 55 Wannan mutumin ba dan masassakin nan ba ne? Ba kuma sunan mahaifiyarsa Maryamu ba? Ba Kuma 'yan'uwansa sune, Yakubu da Yusufu da Saminu da kuma Yahuza ba? 56 Ba 'yan'uwansa mata na tare da mu ba? To daga ina wannan mutumin ya sami dukan wadannnan abubuwa? 57 Suka bata rai saboda shi. Amma Yesu ya ce masu, “Ai annabi bai rasa daraja sai dai ko a garinsa da kuma cikin iyalinsa. 58 Kuma bai yi al'ajibai dayawa a can ba saboda rashin bangaskiyarsu.