14
A lokacin nan ne, Hiridus mai mulki ya ji labarin Yesu. Ya ce wa barorinsa, “Wannan Yahaya mai baftisma ne; ya tashi daga matattu. Saboda haka wadannan ikoki na aiki a cikinsa”. Domin Hiridus ya kama Yahaya, ya daure shi, kuma ya jefa shi a kurkuku saboda Hirudiya, matar dan'uwansa Filibus. Ya ce masa, “Bai kamata ka dauke ta a matsayin matarka ba.” Da Hirudus ya kashe shi, amma yana tsoron jama'a, domin sun dauke shi a matsayin annabi. Amma da ranar bikin haihuwar Hirudus ta kewayo, diyar Hirudiya tayi rawa a lokacin har ta burge Hirudus. Sai ya yi mata alkawari har da rantsuwa cewa ta roki komenene ta ke so, zai ba ta. Bayan ta amshi umurni daga wurin mahaifiyarta, ta ce, “Ka bani kan Yahaya mai baptisma a kan tire. Sarki ya husata da rokonta, amma domin rantsuwar da ya yi kuma domin mutanen da ke a wurin bukin tare da shi, sai ya umurta a yi haka. 10 Ya aika aka yanke kan Yahaya acikin kurkuku. 11 Sai aka kawo kansa bisa tire, aka mika wa yarinyar, ta kuwa kai wa mahaifiyarta. 12 Sai almajiransa suka zo, su ka dauki gawar su ka je su ka yi jana'iza. Bayan haka, su ka je su ka fada wa Yesu. 13 Sa'adda da Yesu ya ji haka, ya fita daga cikin kwale-kwale zuwa wani kebabben wuri. Da taron suka ji haka, suka bi shi da kafa daga biranen. 14 Sai Yesu ya zo gabansu, ya kuma ga babban taron. Ya tausaya masu ya kuwa warkar da marasa lafiya dake cikinsu. 15 Da maraice ya yi, almajiransa su ka zo su ka ce masa, “Wannan wuri jeji ne, dare kuwa ya riga ya yi. Ka sallami taron domin su je cikin kauyukan nan, su sayo wa kansu abinci.” 16 Amma Yesu ya ce masu, “Babu amfanin tafiyar su, ku basu abin da za su ci.” 17 Suka ce masa, “Muna da gurasa guda biyar da kifi biyu ne kawai.” 18 Yesu ya ce, “Ku kawo mani su.” 19 Sai Yesu ya umarci taron su zauna akan ciyawa. Ya dauki gurasa biyar da kifi biyun. Ya dubi sama, ya sa albarka ya gutsuttsura ya kuma ba almajiran. Almajiran suka ba taron. 20 Dukansu suka ci suka koshi. Sai suka dauki gutsattsarin gurasa da kifin, kwanduna goma sha biyu cike. 21 Wadanda su ka ci kuwa kimanin maza dubu biyar ne, ban da mata da yara. 22 Nan take sai ya sa almajiran suka shiga kwale-kwalen su haye zuwa dayan gefen kafin shi, domin ya sallami taron. 23 Bayan ya sallami taron sun tafi, sai ya haura kan dutse domin yayi addu'a. Da dare yayi, yana can shi kadai. 24 Amma yanzu fa kwale-kwalen na tsakiyar tekun, kuma da wuyar sarrafawa saboda rakuman ruwa da iska na gaba da su. 25 Da asuba (wajen karfe uku na dare) Yesu ya nufo su yana tafiya akan teku. 26 Da almajiran suka ganshi yana tafiya akan tekun, sai suka firgita suna cewa, “Fatalwa ce,” suka yi kururuwa cikin tsoro. 27 Amma Yesu yayi magana da su nan da nan yace, “Ku yi karfin hali! Ni ne! Kada ku ji tsoro.” 28 Bitrus ya amsa masa cewa, “Ubangiji, idan kai ne, ka umarce ni in zo wurin ka bisa ruwan.” 29 Yesu yace, “Zo” Sai Bitrus ya fita daga jirgin yana tafiya akan ruwan zuwa wurin Yesu. 30 Amma da Bitrus ya ga iska, sai ya tsorata. Yayin da ya fara nutsewa, sai ya tada murya ya ce, “Ubangiji, ka cece ni!” 31 Nan take Yesu ya mika hannunsa, ya kama Bitrus ya ce masa, “Kai mai karancin bangaskiya, meyasa ka yi shakka?” 32 Bayan da Yesu da Bitrus suka shiga cikin kwale-kwalen, sai iska ta daina kadawa. 33 Sai almajiran dake cikin kwale-kwalen su ka yi wa Yesu sujada suna cewa, “Hakika kai Dan Allah ne.” 34 Da suka haye, sun iso kasar Janisarata. 35 Da mutanen wurin suka gane Yesu, sai suka aika da sako zuwa dukan yankin, kuma suka kawo masa dukan marasa lafiya. 36 Suka roke shi don su taba gezar rigarsa, kuma dukan wadanda suka taba shi sun warke.