3
A kwanakin nan Yahaya Mai baftisma ya zo, yana wa'azi a jejin Yahudiya yana cewa, “Ku tuba, domin mulkin sama ya kusa.” Wannan shine wanda annabi Ishaya ya yi maganarsa, ya ce, “Muryar wani mai kira a jeji yana cewa, 'Ku shirya wa Ubangiji hanyarsa, ku daidaita tafarkunsa.'' Yahaya kuwa yana sanye da tufa ta gashin rakumi, yana kuma daure da damarar fata, abincinsa kuwa fara ne da zuman jeji. Sai mutanen Urushalima, da na dukan Yahudiya, da na duk kasashen bakin Kogin Urdun, suka yi ta zuwa wurin sa. Ya yi masu baftisma a Kogin Urdun, yayinda suke furta zunubansu. Amma da ya ga Farisawa da Sadukiyawa da yawa, suna fitowa domin a yi masu baftisma, sai ya ce masu, “Ku 'ya'yan macizai masu dafi, wa ya gargade ku ku guje wa fushi mai zuwa? Ku ba da 'ya'ya da za su nuna tubanku. Kada kuwa ku dauka a ranku cewa, 'Ibrahim ne ubanmu.' Domin ina gaya maku, Allah yana da iko ya ta da wa Ibrahim 'ya'ya daga cikin duwatsun nan. 10 Ko yanzu ma an sa gatari a gindin bishiyoyin. Saboda haka duk bishiyar da ba ta ba da 'ya'ya masu kyau ba, sai a sare ta a jefa a wuta. 11 Na yi maku baftisma da ruwa, zuwa tuba. Amma mai zuwa baya na, ya fi ni girma, wanda ko takalmansa ma ban isa in dauka ba. Shi ne zai yi maku baftisma da Ruhu Mai Tsarki, da kuma wuta. 12 Kwaryar shikarsa na hannunsa, zai kuwa share masussukarsa sarai, ya tara alkamarsa ya sa a rumbunsa, amma zai kona buntun da wutar da ba za a iya kashewa ba.” 13 Sai Yesu ya zo daga kasar Galili, ya je Kogin Urdun wurin Yahaya, domin ya yi masa baftisma. 14 Amma Yahaya ya yi ta kokarin ya hana shi, yana cewa, “Ni da nake bukatar ka yi mani baftisma, ka zo gare ni?” 15 Yesu ya amsa masa ya ce, “Bari ya zama haka a yanzu, domin a cika dukan adalci.” Sai Yahaya ya yarje masa. 16 Bayan da aka yi masa baftisma, Yesu ya fito nan da nan daga cikin ruwan, sai kuma sammai suka bude masa. Ya ga Ruhun Allah yana saukowa kamar kurciya, ya sauko a kansa. 17 Duba, wata murya daga sammai tana cewa, ''Wannan shi ne kaunataccen Da na. Wanda ya gamshe ni sosai.''