4
1 Sa'an nan Ruhu ya bi da Yesu zuwa cikin jeji, domin Ibilis ya gwada shi.
2 Da ya yi azumi kwana arba'in dare da rana, daga baya yunwa ta kama shi.
3 Sai mai jarabtar nan ya zo, ya ce masa, “Idan kai Dan Allah ne, ka umarci duwatsun nan su zama gurasa.”
4 Amma Yesu ya amsa ya ce masa, “A rubuce yake cewa, 'Ba da gurasa kadai mutum zai rayu ba, sai dai da kowace magana da ta ke fitowa daga wurin Allah.'''
5 Sa'an nan Ibilis ya kai shi tsattsarkan birni ya dora shi can kan kololuwar ginin haikali,
6 ya ce masa, “In kai Dan Allah ne, to dira kasa. Domin a rubuce yake cewa, 'Zai ba mala'ikunsa umarni game da kai,' kuma, 'Za su daga ka da hannuwansu, domin kada ka yi tuntube da dutse.'''
7 Yesu ya ce masa, “kuma a rubuce yake, 'Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.'''
8 Kuma, sai Ibilis ya kai shi kan wani dutse mai tsawo kwarai, ya nuna masa dukan mulkokin duniya da darajarsu.
9 Ya ce masa, “Dukan wadannan zan baka idan ka rusuna ka yi mani sujada.''
10 Sai Yesu ya ce masa, “Tafi daga nan, Shaidan! Domin a rubuce yake, 'Ka yi wa Ubangiji Allahnka sujada, shi kadai za ka bauta wa.'''
11 Sa'an nan Ibilis ya rabu da shi, sai kuma mala'iku suka zo suka yi masa hidima.
12 To, da Yesu ya ji an kama Yahaya, sai ya tashi zuwa kasar Galili.
13 Ya bar Nazarat, ya koma Kafarnahum da zama, can bakin tekun Galili, kan iyakar kasar Zabaluna da Naftali.
14 Wannan ya faru domin a cika fadar annabi Ishaya cewa,
15 “Kasar Zabaluna da kasar Naftali, ta bakin teku, da hayin Kogin Urdun, Galili ta al'ummai!
16 Mutane mazauna duhu suka ga babban haske, sannan ga wadanda ke zaune a yankin da inuwar mutuwa, haske ya keto masu.”
17 Daga lokacin nan, Yesu ya fara wa'azi, yana cewa, “Ku tuba domin mulkin sama ya kusa.”
18 Yana tafiya a bakin tekun Galili, sai ya ga wadansu 'yan'uwa biyu, Saminu da ake kira Bitrus, da dan'uwansa Andarawas, suna jefa taru a teku, domin su masunta ne.
19 Yesu ya ce masu, “Ku zo, ku biyo ni, zan mai da ku masuntan mutane.”
20 Nan da nan sai suka bar tarunsu, suka bi shi.
21 Da Yesu ya ci gaba da tafiya, sai ya ga wadansu mutum biyu, su kuma 'yan'uwa ne, Yakubu dan Zabadi, da dan'uwansa Yahaya, suna cikin jirgi tare da mahaifinsu Zabadi, suna gyaran tarunsu. Sai ya kira su.
22 Nan take suka bar mahaifinsu da jirgin, suka bi shi.
23 Yesu ya zazzaga dukan kasar Galili, yana koyarwa a majami'unsu, yana shelar bisharar mulkin, yana kuma warkar da kowace cuta da rashin lafiya a cikin mutane.
24 Labarinsa ya bazu a cikin dukan kasar Suriya, kuma mutanen suka kakkawo masa dukan marasa lafiya, masu fama da cuta iri iri, da masu shan azaba, da kuma masu aljannu, da masu farfadiya, da shanyayyu. Yesu ya warkar da su.
25 Taro masu yawa suka bi shi daga kasar Galili, da Dikafolis, da Urushalima, da kasar Yahudiya, har ma daga hayin Urdun.