59
Zunubi, furci da kuma fansa
1 Tabbatacce hannun Ubangiji bai kāsa yin ceto ba,
kunnensa kuma bai kurmance da zai kāsa ji ba.
2 Amma laifofinku sun raba
ku da Allahnku;
zunubanku sun ɓoye fuskarsa daga gare ku,
saboda kada yă ji.
3 Gama hannuwanku sun ƙazantu da jini,
yatsotsinku kuma da alhaki.
Leɓunanku suna faɗin ƙarairayi,
harshenku kuma yana raɗar mugayen abubuwa.
4 Babu wani mai ce a yi adalci;
babu wani mai nema a dubi al’amarinsa da mutunci.
Sun dogara a gardandamin banza suna ƙarairayi;
suna ɗaukar cikin ɓarna, su haifi mugunta.
5 Suna ƙyanƙyashe ƙwan kāsā
su kuma saƙa yanar gizo-gizo.
Duk wanda ya ci ƙwansu zai mutu,
kuma sa’ad da ƙwan ya fashe, zai ƙyanƙyashe kububuwa.
6 Yanar gizo-gizonsu ba amfani don tufa;
ba za su iya rufuwa da abin da suka yi ba.
Ayyukansu mugaye ne,
ayyukan tā da hargitsi kuma suna a hannuwansu.
7 Ƙafafunsu sukan gaggauta zuwa aikata zunubi;
suna da saurin zub da jini.
Tunaninsu mugaye ne;
lalaci da hallaka sun shata hanyoyinsu.
8 Ba su san hanyar salama ba;
babu adalci a hanyoyinsu.
Sun mai da su karkatattun hanyoyi;
babu wanda zai yi tafiya a kansu ya sami salama.
9 Saboda haka gaskiya ta yi nisa da mu,
adalci kuma ba ya kaiwa gare mu.
Muna neman haske,
sai ga duhu;
muna neman haske, sai muka yi ta tafiya cikin baƙin inuwa.
10 Kamar makafi, sai lallubar bango muke yi,
muna lallubawar hanyarmu kamar marasa idanu.
Da tsakar rana muna tuntuɓe sai ka ce wuri ya fara duhu;
cikin ƙarfafa, mun zama kamar matattu.
11 Muna gurnani kamar beyar;
muna ta ƙugi kamar kurciyoyi.
Muna ta neman adalci amma ina;
mun nemi fansa, amma yana can da nisa.
12 Gama laifofinmu suna da yawa a gabanka,
zunubanmu kuma suna ba da shaida gāba da mu.
Laifofinmu kullum suna a gabanmu,
muna kuma sane da laifofinmu,
13 tawaye da mūsun Ubangiji,
mun juye bayanmu ga Allahnmu,
zugawa a yi zalunci da tayarwa,
faɗin ƙarairayi da zukatanmu suka shirya.
14 Saboda haka aka kau da yin gaskiya
adalci kuma ya tsaya can da nesa;
gaskiya ta yi tuntuɓe a tituna,
sahihanci ba zai shiga ba.
15 Gaskiya ta ɓace gaba ɗaya,
kuma duk wanda ya guji mugunta zai zama ganima.
Ubangiji ya duba bai kuwa ji daɗi
cewa babu adalci ba.
16 Ya ga cewa babu wani,
ya yi mamaki cewa babu wanda zai shiga tsakani;
saboda haka hannunsa ya aikata masa ceto,
adalcinsa kuma ya raya shi.
17 Ya yafa sulke a matsayin rigar ƙirji,
da hulan kwanon ceto a kansa;
ya sa rigunan ɗaukar fansa
ya kuma nannaɗe kansa da kishi kamar a cikin alkyabba.
18 Bisa ga abin da suka yi,
haka za a sāka
fushi a kan abokan gābansa
ramuwa kuma a kan maƙiyansa;
zai sāka wa tsibirai abin da ya dace da su.
19 Daga yamma, mutane za su ji tsoron Ubangiji,
daga mafitar rana kuma, za su girmama ɗaukakarsa.
Gama zai zo kamar rigyawa mai tsananin gudu
cewa numfashin Ubangiji zai tafi tare da shi.
20 “Mai fansa zai zo Sihiyona,
zuwa waɗanda suke cikin Yaƙub da suka tuba daga zunubansu,”
in ji Ubangiji.
21 “Game da ni dai, ga alkawarina da su,” in ji Ubangiji. “Ruhuna, wanda yake a kanka, da kuma maganata da na sa a bakinka ba za tă rabu da bakinka ba, ko daga bakunan ’ya’yanka ba, ko kuwa daga bakunan zuriyarsu ba daga wannan lokaci zuwa gaba da kuma har abada,” in ji Ubangiji.