Zabura 134
Waƙar haurawa.
Yabi Ubangiji, dukanku bayin Ubangiji
waɗanda kuke hidima da dare a gidan Ubangiji.
Ku tā da hannuwanku a cikin wurinsa mai tsarki
ku kuma yabi Ubangiji.
 
Bari Ubangiji, Mahaliccin sama da ƙasa,
ya albarkace ku daga Sihiyona.