Zabura 4
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da kayan kiɗi masu tsirkiya. Ta Dawuda.
Ka amsa mini sa’ad da na kira gare ka,
Ya Allahna mai adalci.
Ka ba ni sauƙi daga wahalata;
ka ji tausayina ka kuma ji addu’ata.
 
Har yaushe, ya ku mutane za ku mai da ɗaukakata abin kunya?
Har yaushe za ku ƙaunaci ruɗu ku nemi allolin ƙarya?
Sela
Ku san cewa Ubangiji ya keɓe masu tsoron Allah wa kansa;
Ubangiji zai ji sa’ad da na yi kira gare shi.
 
Cikin fushinku kada ku yi zunubi;
sa’ad da kuke kan gadajenku,
ku bincike zukatanku ku kuma yi shiru.
Sela
Ku miƙa hadayun da suka dace
ku kuma dogara ga Ubangiji.
 
Yawanci suna cewa, “Wa zai yi mana alheri?”
Bari hasken fuskarka yă haskaka a kanmu, ya Ubangiji.
Ka cika zuciyata da farin ciki
sa’ad da hatsinsu da sabon ruwan inabinsu ya yi yawa.
 
Zan kwanta in kuma yi barci lafiya,
gama kai kaɗai, ya Ubangiji,
kake sa mazaunina yă kasance lafiya lau.