Zabura 5
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Don Busa. Ta Dawuda.
Ka saurare kalmomina, ya Ubangiji,
ka ji ajiyar zuciyata.
Ka saurare kukata na neman taimako,
Sarkina da Allahna,
gama gare ka nake addu’a.
 
Da safe, ya Ubangiji, ka ji muryata;
da safe na gabatar da bukatuna a gabanka
in kuma jira da sa zuciya.
Kai ba Allahn da yake jin daɗin mugu ba ne;
gama kana gāba da dukan masu aikata mugunta.
Masu fariya ba za su iya tsaya
a gabanka ba.
Kana ƙin duk masu aikata abin da ba daidai ba.
Kakan hallaka masu yin ƙarya.
Masu kisankai da mutane masu ruɗu
Ubangiji yana ƙyama.
Amma ni, ta wurin jinƙanka mai girma,
zan shiga gidanka;
da bangirma zan durƙusa
ga haikalinka.
 
Ka bi da ni, ya Ubangiji, cikin adalcinka
saboda abokan gābana,
ka fayyace hanyarka a gabana.
Babu ko kalma guda daga bakinsu da za a dogara da ita;
marmarinsu kawai shi ne su hallakar da waɗansu.
Maƙogwaronsu buɗaɗɗen kabari ne;
da harshensu suna faɗin ƙarya.
10 Ka furta su masu laifi, ya Allah!
Bari makircinsu yă zama fāɗuwarsu.
Ka kore su saboda yawan zunubansu,
saboda sun tayar maka.
11 Amma bari dukan waɗanda suke neman mafaka gare ka su yi murna;
bari kullum su yi ta rerawa saboda farin ciki.
Ka buɗe kāriyarka a bisansu,
domin waɗanda suke ƙaunar sunanka su yi farin ciki a cikinka.
 
12 Gama tabbatacce, ya Ubangiji, kakan albarkaci adalai;
kakan kewaye su da tagomashinka kamar garkuwa.