Zabura 6
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da kayan kiɗi masu tsirkiya. Bisa ga sheminit. Ta Dawuda.
1 Ya Ubangiji, kada ka tsawata mini cikin fushinka
ko ka hore ni cikin hasalarka.
2 Ka yi mini jinƙai, Ubangiji, gama na suma;
Ya Ubangiji, ka warkar da ni, gama ƙasusuwana suna zafin ciwo.
3 Raina yana cikin wahala.
Har yaushe, ya Ubangiji, har yaushe?
4 Ka juyo, ya Ubangiji, ka cece ni;
ka cece ni saboda madawwamiyar ƙaunarka.
5 Babu wanda yakan tuna da kai sa’ad da ya mutu.
Wa ke yabonka daga kabari?
6 Na gaji tiƙis daga nishi.
Dukan dare na jiƙe gadona da kuka
na jiƙe kujerata da hawaye.
7 Idanuna sun rasa ƙarfi da baƙin ciki;
sun rasa ƙarfi saboda dukan abokan gābana.
8 Ku tafi daga gare ni, dukanku masu aikata mugunta,
gama Ubangiji ya ji kukata.
9 Ubangiji ya ji kukata saboda jinƙansa;
Ubangiji ya karɓi addu’ata.
10 Dukan abokan gābana za su sha kunya su kuma karaya;
za su juya da kunya nan da nan.