Zabura 96
Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji;
ku rera ga Ubangiji, ku duniya duka.
Ku rera ga Ubangiji, ku yabe sunansa;
ku yi shelar cetonsa kowace rana.
Ku furta ɗaukakarsa a cikin al’ummai,
manyan ayyukansa a cikin dukan mutane.
 
Gama da girma Ubangiji yake, ya kuma cancanci yabo;
tilas a ji tsoronsa fiye da dukan alloli.
Gama dukan allolin al’ummai gumaka ne,
amma Ubangiji ne ya yi sammai.
Daraja da ɗaukaka suna a gabansa;
ƙarfi da ɗaukaka suna a cikin tsarkakar wurinsa.
 
Ku ba wa Ubangiji, ya iyalan al’ummai
ku ba wa Ubangiji ɗaukaka da kuma ƙarfi.
Ku ba wa Ubangiji ɗaukakar da ta dace da sunansa;
ku kawo sadaka ku kuma zo cikin filayen gidansa.
Ku bauta wa Ubangiji da darajar tsarkinsa;
ku yi rawar jiki a gabansa, dukan duniya.
10 Ku faɗa cikin al’ummai, “Ubangiji yana mulki.”
Duniya ta kahu daram, ba za a iya matsar da ita ba;
zai yi wa mutane hukunci da gaskiya.
 
11 Bari sammai su yi farin ciki, bari duniya tă yi murna;
bari teku tă yi ruri, da kuma dukan abin da yake cikinsa;
12 bari gonaki su yi tsalle da murna, da kuma kome da yake cikinsu.
Ta haka dukan itatuwan kurmi za su rera don farin ciki;
13 za su rera a gaban Ubangiji, gama yana zuwa,
yana zuwa don yă hukunta duniya.
Zai hukunta duniya cikin adalci
mutane kuma cikin amincinsa.