Zabura 97
Ubangiji yana mulki, bari duniya tă yi murna;
bari tsibirai masu nesa su yi farin ciki.
Gizagizai da baƙin duhu sun kewaye shi;
adalci da gaskiya su ne tushen kursiyinsa.
Wuta tana tafiya a gabansa
tana kuma cinye maƙiyansa a kowane gefe.
Walƙiyarsa ta haskaka duniya;
duniya ta gani ta kuma yi rawar jiki.
Duwatsu sun narke kamar kakin zuma a gaban Ubangiji,
a gaban Ubangijin dukan duniya.
Sammai sun yi shelar adalcinsa,
dukan mutane kuma suka ga ɗaukakarsa.
 
Dukan waɗanda suke bauta wa siffofi sun sha kunya,
waɗanda suke fariya da gumaka,
ku yi masa sujada, dukanku alloli!
 
Sihiyona ta ji ta kuma yi farin ciki
kuma dukan ƙauyukan Yahuda suna murna
saboda hukunce-hukuncenka, ya Ubangiji.
Gama kai, ya Ubangiji, kai ne Mafi Ɗaukaka a bisa dukan duniya;
ana darjanta ka fiye da dukan alloli.
10 Bari masu ƙaunar Ubangiji su ƙi mugunta,
gama yana tsaron rayukan amintattunsa
yana kuma kuɓutar da su daga hannun mugaye.
11 An haskaka haske a kan masu adalci
da kuma farin ciki a kan masu gaskiya a zuciya.
12 Ku yi farin ciki a cikin Ubangiji, ku da kuke masu adalci,
ku kuma yabi sunansa mai tsarki.